Zan Daure Barayi Da Yawa - Buhari
- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa aiki daga hutu shi ne daure barayi.
Muhammad Buhari ya bayyana haka ne a hirar sa da gidan talbijin na NTA jim kadan bayan ya isa fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Bayan da aka tambaye shi game da abin da zai sa a gaba bayan ya yi hutun kwana goma, Shugaba Buhari ya ce "za mu daure barayi da yawa wadanda suka jefa mu cikin matsin tattalin arziki. Da ma na san ana sa ran zan yi hakan, kuma zan yi."
Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa lokacin da yake yakin neman zabe.
Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya ya rasu
Comments