Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Kama Wani Da Ya Kware Wajen Kera Bindigogi Yana Siyarwa Yan Fashi

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da kama, Rabi'u Sulaiman, da ya kware wajen kera bindigogi yana sayarwa Yan fashin dake addabar jama'a a dajin falgore da titin Kano-Zaria-Kaduna.
Kakakin Yan sandan ya rubuta a shafin Sa na facebook kamar haka "
Wannan shine Rabiu Suleman Mutumin Kauyen Fadan Yalwa dake Karamar Hukumar Tudun Wada, shi kwararre ne wajen kera bindiga kala-kala yana sayarwa da Yan fashi dake addabar Jama’a a Dajin Falgore da Titin Kano-zuwa Zaria da Kaduna da sauran yankunan kudancin Kano. Mun kama shi da bindigogi da harsashi mai yawa kuma ana cigaba da gudanar da bincike".
Shiga shafin mu na Facebook

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Tsohon gwamnan jahar Gombe Abubakar Hashidu ya rasu

Cristiano Ronaldo ya hadu da abokan wasan sa na Juventus a karon farko

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Tsohon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan, Ya Rasu