An Kama Manyan Dillalan Miyagun Kwayoyi Hudu A Jihar Gombe

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, Shina Olukolu, ya bayyana cewa dakarun sa sun kama wasu dillalen miyagun kwayoyi hudu a jihar.

Olukolu ya fadi haka ne ranar Alhamis a garin Gombe inda ya kara da cewa rundunar ta kama wadannan mutanen da miyagun kwayoyi da yawa a tare da su.
Ya ce bayanan da suka samu game da su wadannan mutane ne ya sa suka sami nasarar kama su.
” Cikin kwayoyin da muka kama su da shi sun hada da kwayoyin Tramadol, Vallium, Dizapam, Exzol, Kodin da madaran su kodai’’.
A karshe, Olukolu ya ce za su gurfanar da su a kotu da zaran an kammal bincike a kan su.

Shiga Facebook din mu

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP