Cutar kwalara da ta barke a Jamhuriyyar Nijar inda ta hallaka kusan mutane 19.

Kimanin mutane dubu 1,168 ne suka kamu da cutar a gundumar Madarunfa ta jahar Maradi da ke yankin kudancin kasar.
Sama da wata daya ke nan da aka samu barkewar wannan cuta a wannan yanki, kuma cikin wadanda lamarin da cutar ya shafa yara kanana sun fi yawa.
Dr Alhaji Ibrahim Tasiu shi ne darakatan kiwon lafiya a gundumar ta Madarunfa kuma ya shaidawa BBC cewa daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa yanzu kusan mutane 19 suka mutu.
Mutanen da suka kamu da wannan cuta ta amai da gudawa na kwance a babban asibitin birnin Maradi ne, kamar yadda hukumar jin kai ta Majalasar Dinkin Duniya wato OCHA ta sanar.
Rahotanni sun bayyana cewa a garin N'Yelwa ne aka fara samun mutum na farko da ya kamu da cutar tun a farkon watan Yuli da ya wuce.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP