Jami'ar Bayero ta Kano ta kori dalibai talatin da uku akan samun su da magudin jarrabawa

     
Hukumomin jami'ar Bayero ta Kano sun kori dalibai talatin da uku saboda zargin shigarsu cikin hanyoyi daban-daban na magudin jarrabawa a yayin jarrabawar zangon farko na shekarar 2017/18.
Bayani da yake kunshe da sa hannun mukaddashin darakta akan jarrabawa da ajiye bayanai, Hajiya Amina Abdullahi, ya tabbatar da amincewar hukumar dattijan jami'ar na korar daliban da abin ya shafa.

Jami'ar ta ce dalibai coma sha biyu za su maimaita shekarar karatun, saba' in da biyu kuma an gargade su. " Haka kuma, an wanke dalibai biyu daga kowanne laifi, yayin da dalibai biyu kuma a jingine hukunta su har said an kammala bincike.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP