Kada Ku Sassauta Wa 'Yan Ta'adda - Sakon Buhari Ga Sojoji

      Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bukaci sojojin kasar da kada su sasauta wa 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma masu satar dabbobi. Shugaban ya bayyana haka ne a yau Asabar a filin jirgin saman Katsina lokacin da yake ganawa da sojojin gabanin komawarsa Abuja bayan ya yi hutun babbar sallah a mahaifarsa dake Daura.
Sojojin na cikin rundunar Operations Sharan Daji da Diran Mikiya wadanda aka tura jihar Zamfara da makwabtan jihohi domin magance matsalar barayin mutane da shanu da kuma 'yan fashi da makami.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP