Shin Farfesa Osinbajo zai zama shugaban Najeriya?

A halin yanzu 'yan Nijeriya da dama na nuna wa mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo matukar so irin wanda ba kasafai 'yan siyasa ke samu ba, a kasar da ba a kallon galibin 'yan siyasa da kima sosai.
Ana yaba wa mataimakin shugaban kasar saboda yadda ya dauki kwararan matakai ba tare da wata-wata ba yayin da ya rika wa Shugaba Buhari a matsayin mukaddashin shugaban Nijeriya, lokacin hutun shugaban na kwanaki goma a baya-bayan nan.
Yanayin hobbasa da kazar-kazar din mutumin, mai shekaru 61 a duniya, ya sha bamban da yanayin jinkiri da jan-kafa na Shugaba Buhari, mai shekaru 75 a duniya, wanda wasu 'yan kasar ke wa lakabi da ''Baba Go-slow'', wato ''Baba Mai nawa.''
Manyan jami'an gwamnatin Najeriya dai na cewa duk wani mataki da mataimakin shugaban kasar ko kuma shi kansa Shugaba Buhari ya dauka, abu ne na gwmnati guda babu wani bambanci, kuma dukkanninsu sun zo ne da manufofi guda da zimmar aiki tare.
Amma duk da haka wasu sun fara kwatanta salon jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da na mataimakin nasa Osinbajo.
'Halayyar azabtarwa da muguntar 'yan sanda'
Matakin na baya-bayan nan da Farfesa Osinbajo ya dauka shi ne bayar da umarnin a yi garambawul ga sashen nan na rundunar 'yan sanda da aka kirkiro domin yaki da fashi da makami da satar mutane da ake kira SARS a takaice, wanda ya yi kaurin suna a wajen 'yan Najeriya.
Mukaddashin shugaban ya kuma umarci Hukumar Kare Hakkin bil-Adama ta Kasar da ta gudanar da bincike game da ayyukan keta hakkin bil-Adama da ake zargin jami'an SARS sun aikata ko suna aikatawa.
An dai kwashe fiye da shekara guda ana matsa wa Shugaba Buhari lamba don ya dauki mataki a kan sashen 'yan sandan na SARS, yayin da aka yada labarai da rahotanni a shafukan sada zumunta da wasu kafofin labarai na irin ayyukan assha da ake zargin ma'aikatan na SARS da aikatawa.
Zarge-zarge sun hada da azabtarwa, da kashe-kashen mutane ba tare da shari'a ba, da kuma kama mutane gami da tsare su ba bisa ka'ida ba, da kuma tatsar kudi daga jama'a da dai wasu nau'o'i na mugunta.
Cikin masu wadannan zarge-zarge har da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International.
An kuma kaddamar da wata fafutika ta shafukan sada zumunta mai taken #EndSars tare da kiraye-kirayen a rusa sashen na SARS.
Farfesa Osinbajo ya ce ya dauki mataki ne saboda ''yadda jama'a ke ci gaba da koke-koke babu kakkautawa da kuma rahotanni game da ayyukan Sashen na Musamman don Yaki da Fashi (SARS), wadanda suka shafi zarge-zargen keta hakkokin bil-Adama.''
Me ya faru a Nigeria tun da Shugaba Buhari ya tafi hutu?
Ba ni da niyyar tsayawa takara a 2019 — Osinbajo
Bai dai rusa sashen na 'yan sanda ba amma ya ce a yi garambawul kuma su mayar da hankali wajen aiki da bayanan sirri, kuma kada su wuce gona da iri a ayyukan da aka ba su na yaki da fashi da kuma satar mutane domin neman kudin fansa.
Haka nan kuma wajibi ne jami'an 'yan sandan na SARS su makala shaidar ko su wane ne karara yayin da suke aiki, abin da zai taimaka wajen gane duk jami'in da ya aikata ba daidai ba.
'Yan Najeriya da dama sun bayyana farin cikinsu da hakan a Twitter, kuma ga alama sun ji dadin ganin yadda wani dan siyasa ke daukar mataki babu inda-inda.

Sallamar Shugaban DSS Lawal Daura
Kafin daukar matakin yi wa SARS garambawul, Farfesa Osinbajo ya kuma dauki gagarumin mataki na ba-zata na sallamar shugaban hukumar 'yan sandan ciki ta Najeriya, Lawal Musa Daura, wani mutum mai janyo ce-ce-ku-ce. Matakin ya biyo bayan killace ginin Majalisar Dokoki ta Najeriya ne da jami'an tsaro sanye da hulunan dodo suka yi, daga bisani kuma bayanai suka nuna cewa jami'an hukumar tsaron ta DSS ne.
Lamarin garkame kofar majalisar ya daure wa mutane da dama kai - kuma har yanzu babu cikakken bayani kan dalilan kutsen, amma masu lura da lamaru na danganta lamarin da makirce-makircen siyasa gabanin zabukan da ake shirin yi a watan Fabrairu.
Ko ma dai mene ne dalili, 'yan Najeriya da dama sun dade suna kallon shugaban hukumar 'yan sandan cikin ta Najeriya, Lawal Daura, a matsayin daya daga cikin mutanen da ke janyo wa gwamnatin Buhari bakin jini da kuma zubar mata da kima a idanun jama'a saboda wuce gona da iri da ake zargin jami'an hukumar da yake shugabanta na yi.
Masu suka da dama sun kasa fahimtar abin da ya sa Shugaba Buhari - wanda shi ya nada Lawal Daura - ya kasa daukar mataki a kansa.
A wani lamari mai kama da hannun riga da yanayin Shugaba Buhari, mataimakinsa Farfesa Osinbajo, a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasa, bai bata lokaci ba wajen tarar aradu da ka kana ya bayyana take-taken Lawal Daura a matsayin ''abubuwan ba za a amince da su ba, kuma sun saba tsarin doka da oda.''
Sosa wa jama'a wurin da ke masu kaikayi
Farfesa a fannin shari'a, mataimakin shugaban na Najeriya ba sasanne mutum ne a fadin Najeriya ba kafin ya zama mataimakin Shugaba Muhammadu Buhari, amma wadanda suka san shi suna bayyana shi a matsayin mutum mai kwazo da shiru-shiru.
Amma mutum ne mai zalaka wajen magana, kuma mai fara'a da kuma tausayi.
Ya kasance kwamishinan Shari'a a jihar Legas daga 1999 zuwa 2007 inda ya kawo sauye-sauye a fannin shari'a ciki har da kirkiro wani sashe na musamman domin kare hakkin bil-Adama.
Ya kuma kasance Fasto mai shugabantar majami'ar Redeemed Christian Church of God a birnin Legas.
A 2015 ya zama mataimakin shugaban kasa, lokacin da shugaba Buhari ya tsallake dukkan shingayen da ake jin ba a iya tsallakewa a siyasar Najeriya inda ya doke shugaba da ke kan karagar mulki a wancan lokacin wato Goodluck Jonathan a zabe, kana ya zama shugaban Najeriya.
Daga lokaci zuwa lokaci, Osinbajo kan rike ragamar Najeriya a matsayin mukaddashin shugaban kasa.
Ana dai yaba wa shugaba Buhari saboda yadda yake bin tanadin kundin tsayin mulki na mika ragama ga mataimakinsa yayin da zai yi hutu, sabanin yadda aka saba gani a baya yadda wasu shuwagabannin ba su yin haka.
A shekarar 2017 lokacin da shugaba Buhari ya tafi hutun neman magani a London, mataimakin nasa ya dauki wasu matakai na gyara tattalin arzikin kasa da nufin tallafa wa darajar kudin kasar wato Naira.
A lokacin ana fama da karancin dala wadda 'yan kasuwa masu sayo kaya daga kasashen waje ke bukata, don haka sai ya nemi Babban Bankin Najeriya, CBN, ya zuba miliyoyin dala a kasuwa domin daidaita darajar Naira wacce a lokacin ke ci gaba da faduwa warwas.
Farfado da tattalin arzikin kasa na daya daga cikin alkawuran yakin neman zabe na shugaba Buhari, to amma masana na cewa kawo yanzu bai aiwatar da irin manyan sauye-sauye da ake bukata ba.
Ga alama Farfesa Osinbajo ba ya so a kalle shi a matsayin mai taka rawar-gaban-hantsi, kuma kullum yana jaddada biyayyarsa ga mai gidan nasa Buhari.
Hasali ma, cewa yake yi ba ya daukar duk wani mataki ba tare da ya tuntubi shugaba Buhari da kuma samun amincewarsa ba - don haka, da kai da kaya duka mallakar wuya ne.
Duk da yana nuna cewa manufofin gwamnatinsu guda ne, kuma duk matakan da aka dauka da sunan gwamnatin Buhari aka dauke su, to amma salon shugabancinsa ya soma jawo masa masoya da dama.
Wasu dai na cewa Farfesa Osinbajo mutum ne mai saurin fahimtar inda ra'ayin jama'a ya fi karkata, da kuma sosa wa jama'a wurin da yake masu kaikayi nan take - ba tare da bata lokaci.
Me ya sa salon daukar matakin Osinbajo ya sha bamban
da na Buhari?
Wasu dai na da ra'ayin cewa daya daga cikin dalilan salon hobbasa da kazar-kazar na mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, mai shekaru 61 da haihuwa, shi ne bai da manyan mukarrabai da dama masu karfin fada a-ji, don haka yana da 'yanci da kuma damar daukar mataki bisa tunaninsa na abin da ya dace ba tare da wasu mukarrabai sun sauya masa ra'ayi cikin sauki ba.
A daya bangaren kuma, mai gidansa Shugaba Buhari da kyar yake iya daukar mataki na ladabtar da jami'an gwamnati musamman mukarrabansa masu fada a-ji, kuma ba ya iya kawo sauye-sauye a cibiyoyi da hukumomin gwamnati cikin hanzari.
Haka zalika, wasu na ganin kuzarin da Farfesa Osinbajo ke nunawa ba zai rasa nasaba da karancin shekarunsa, idan aka kwatanta da shugaba Buhari mai shekaru 75.
Wasu masu lura da lamura kuma na ganin rashin adalci ne a kwatanta mutanen biyu domin rike ragamar shugabanci na 'yan makwanni ko watanni ba daidai yake ba da shugabanci na cikakken wa'adin mulki musamman a kasa wacce take bambarakwai, inda kuma galibin shuwagabanni kan gaza ko kuma su yi ta tafka kurakurai idan tafiya ta yi nisa.
Najeriya, wadda tafi kowace kasa a Afirka yawan jama'a, kasa ce mai wuyar sha'ani da sarkakiya, kuma daidaita bukatu da muradu daban-daban - ta fuskar bambancin siyasa, da kabila, da addini da kuma yankunan kasa - ba karamin aiki ba ne.
Yayin da 'yan Nijeriya da dama ba su da tababa ko shakku kan gaskiyar Shugaba Buhari da kishin kasarsa, da kudurinsa da kuma burinsa na magance tarin matsalolin kasar, suna kuma cewa wasu daga cikin mukarrabansa mutane ne masu son zuciya, wadanda ba su sanya muradun kasar gaba da muradunsu na kashin kai.
Haka nan kuma larurar rashin lafiya da ya fuskanta a bara ta kawo cikas ga kuzari da azamarsa, da kuma kwazonsa, ko da yake dai a baya-bayan nan alamomi na nuna cewa lafiyar tasa ta inganta kwarai.
Duk da irin sukar da Shugaba Buhari ke sha saboda jinkirinsa wajen daukar mataki, mutane da dama na yaba wa da kokarinsa wajen yaki da cin hanci da rashawa, da yaki da masu tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram, da yunkurinsa na fadada tattalin arzikin kasa musamman fannin noma, da kuma kyautata martabar Najeriya a idanun duniya.
Ya kama hanyar zama shugaban Najeriya?
Yanzu dai watanni suka rage a gudanar da manyan zabuka a Najeriya, kuma wasu 'yan kasar sun fara tunanin yadda lamura za su kasance idan Farfesa Osinbajo ya kasance cikakken shugaban Najeriya ta yin la'akari da irin matakan da ya dauka a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasa.
Tuni dai shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta neman wa'adin mulki na biyu a zaben tare da sake ayyana Farfesa Osinbajo a matsayin mataimakinsa a inuwar jam'iyyar APC.
Haka zalika akwai tsarin da ake bi a Najeriya na karba-karbar shugabanci tsakanin Kudu da Arewa bayan wa'adi biyu-biyu bisa fahimtar juna - amma ba tanadi na dokokin kasa ba.
Ana ganin dai wannan karon na Arewa ne.
Shugaba Buhari, wanda dan arewa ne, yana kokarin kammala wa'adin mulkinsa na farko ne yanzu, don haka da wuya mataimakin nasa mai biyayya, Farfesa Osinbajo, wanda dan kudancin kasar ne, ya yi takarar shugabancin kasar a wannan karon.
Shi ma mataimakin shugaba kasa Osinbajo bai nuna sha'awarsa ta neman shugabancin Najeriya ba.
Wani lamarin kuma shi ne su ma 'yan adawa na da damar samun nasara a zaben, lamarin da ka iya kawar da Farfesa Osinbajo da maigidan nasa Buhari daga fagen mulki.
Yayin da bisa dukkan alamu zai yi wuya Farfesa Yemi Osinbajo ya zama cikakken shugaban Najeriya a nan kusa, amma wasu na ganin yana da dama a shekaru da ke tafe, kuma a siyasar Najeriya komai ka iya yiwuya.
Rahoton Ishaq Khalid Abuja, BBC Hausa.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019