Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mai da martani akan ajiye aikin da mataimakin sa, Hafizu Abubakar, yayi.
 Ya bayyana cewa akwai zargi akan tsohon mataimakin nasa na kashe sama da naira miliyan dari da hamsin akan tafiye-tafiyen kasashen ketare da na cikin gida.
Ganduje ya ce mataimakin nasa ya ajiye aiki ne dan gudun shirin tsige shi da talatin cikin arba'in na 'yan majalisar za su yi masa saboda zarge-zarge da kuma cin dunduniyar gwamnatin ta Kano.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP