Roman Abramovich Ya Sa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea A Kasuwa

Jaridar Sunday times sun ruwaito cewa mamallakin kungiyar kwallon kafa ta chelsea, Roman Abramovich, ya hayo wani banki dake New York mai suna 'Raine Group' dan yayi masa dillanci akan shirin sa na sayar da kulob din.

Bankin dai an ce yayi ma kulob din kiyasin kudi £2billion (Naira tiriliyan 840). Abramovich ya sayi Chelsea din a 2003 akan kudi £140 million (Naira biliyan 58.8).

Sune kulob din London na farko da ya dau kofin zakarun turai a shekarar 2012.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP