Illar Shan Magunguna Barkatai

Abin da ya kamata ka sani dangane da shan magungunan ciwon jiki barkatai.
__________________
Ɗabi'ar shan magungunan ciwon jiki da gaɓɓai ɗabi'a ce da ta zama ruwan dare, sai dai jinsin magungunan rage ciwo, raɗaɗi, ko zafin jiki da ake cewa NSAIDs (Nonsteroidal Anti-inflammatory Drugs) ba sune mafita ga masu fama da ciwon jiki ba, kamar masu fama da ciwon baya, ciwon wuya, ciwon gwiwa da sauransu.
Domin irin waɗannan ciwuka suna faruwa ne sakamakon saɓanin zaman ƙashi, jijiya da tsoka a jiki.
Saboda haka ciwon jiki ko ciwon wata gaɓa na faruwa ne a matsayin alama ko gargaɗi cewa an sami saɓani tsakanin tsoka, ƙashi ko jijiya. Wannan ne yasa ko mutum ya sha maganin ciwon jiki da zarar ƙarfin maganin ya ƙare a cikin jini to wannan ciwo zai dawo har sai an sake shan wani maganin kuma.
A taƙaice jinsin waɗannan magunguna ba sune haƙiƙanin matsalar ciwo ba dangane da ciwukan jiki da suke da asali daga jijiya, ƙashi da tsoka. Haka nan waɗannan magunguna suna a matsayin shamaki ne tsakanin ciwo da mai jin ciwo na wani ƙayyadajjen lokaci amma ba a matsayin amsa ga asalin matsalar da ta haifar da ciwon ba.
Domin haka matuƙar ba a gyara ko daidaita saɓanin da ke tsakanin jijiya, ƙashi da tsoƙa ba to wannan ciwo zai cigaba duk da shan waɗannan magunguna.
Bugu da ƙari, dangane da illar da shan magungunan barkatai kan haifar ga lafiya jikin mutum kuwa, masana magunguna sun tabbatar da cewa shan magungunan barkatai na da illar gaske akan ƙoda da kuma haifar da matsalar gyamban ciki da dai sauransu.
Ina Mafita?
1) Mafita ta farko daga waɗannan matsaloli ita ce ƙauracewa shan waɗannan magunguna ba tare da sahalewar likita ba.
2) Mafita ta biyu ita ce daidaita ko gyara wancan saɓanin da ke tsakanin jijiya, ƙashi ko tsoka da ya haifar da ciwon. Maganin matsalar daga asalinta ne zai maganin ciwon daga tushe.
Likitocin Physiotherapy sune ke da ƙwarewar daidaita matsalolin da suke haifar da ciwukan jiki da gaɓɓai.
Ƙauracewa shan magungunan ciwon jiki barkatai domin lafiyar ku.
Tuntuɓi likitan Physio a yau!
https://mobile.facebook.com/PhysioHausa

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP