'Zan Tsaya Takarar Shugaban K'asa A 2019 Idan 'Yan Najeriya Suka Bukaci Hakan — Hamza Al-Mustapha

Tsohon dogarin Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewar zai iya tsayawa takarar shugaban 'kasar Najeriya a 2019 idan har 'yan Najeriya sun bu'kaci ya fito takara.
"Ba zan bada sanarwar cewa zan yi takarar kujerar shugaban 'kasa ba. Amma idan mutane suka ce haka, to hakan shi ne muradinsu," Al-Mustapha ya faɗa a wata tattaunawa da aka yi da shi a Kaduna, bayan wani taro da ya yi da shuwagabannin wata 'kungiya mai rokonsa da ya tsaya takarar shugaban 'kasa a 2019 mai suna 'Eagle Eye Forum'.
Al-Mustapha ya 'kara da faɗin: "Ni ba mutum ba ne mai matu'kar kwaɗayin mulki. Da ni mutum ne mai kwaɗayin hakan da tun a baya na rasa mutuncina. Amma idan mutane suka taru domin su yi magana, sannan suka yanke shawara da kansu, to wannan kira ne domin hidimta wa 'kasa."

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019