Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana komawar sa jam'iyyar PDP daga jam'iyyar APC.
Tsohon shugaban majalisar tarayyar ya bayyana komawar sa ne a gaban dandazon magoya bayan sa a fadar gwamnatin jihar Sokoto.
Gwamnan ya bayyana cewa a shirye yake don ganin Jam'iyyar PDP ta samu nasara a dukkanin matakan zabuka a shekarar 2019.
Manyan yan siyasa na ta barin jam'iyyar APC

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu