LAIFIN KWANKWASO 'DAYA !!!

   Ra'ayin Alhaji Sharif Hifzullah

Laifin Kwankwaso daya dai shi ne ya nemi kujerar Buhari. Maganar zargin sata kuwa, idan ka cire Buharin, babu wanda ba'a zargin sata akansa har da muqarraban Buharin.
Amma idan ka natsu da kyau, ka dubi yadda Kwankwaso ya tura 'ya'yan talakawa da ya tura karatu, wadanda tuni suka fita qangin talauci da zaman banza, zaka iya cewa tun daga Sardauna, ba'a qara samun mai kishin Arewa ba kamar Kwankwaso.
A lokacin da aka kama masu farauta daga Jigawa a garin Imo, ana zarginsu da zama 'yan Boko Haram, a 2014, Kwankwason dai ya kai masu dauki. Wataqila da har yanzu suna can garqame ko kuma ankashe su. Haka ya yi tattaki har zuwa Ile-Ife inda ake kashe Hausawa a garin. Ya kuma je Mile 12 a lokacin da aka kashe Hausawa. Zuwansa Ile Ife ya sanya duk wadanda ake zargi akan rikicin aka mayar da su a Abuja domin yi masu shari'a.
A yanzu, Yarabawa sun fi kowa amfana da wannan gwamnatin ta Buhari a fannin ayyukan titi, hanyoyin jirgin qasa da dai sauransu duk kuwa da cewar Arewa ce koma baya a wadannan ayyukan.
Yana da kyau mu samu second option musamman tun da daga 2019, Kwankwaso yana da kishin Arewa kuma idan ya samu dama, Arewa zata iya samun taimakon yin kafad'a da kafad'a da sauran sassan kasarnan.
Kafin ka zagi Kwankwaso, ka fara duba abinda ya yiwa Kano da nigeria baki daya..

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP