Kwankwaso Ya Hadu Da Matukin Jirgin Sama Da Ya Dauki Nauyin Karatun Sa A Hanyar Sa Ta zuwa Abuja

Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya hau jirgin saman Azman yau da safe daga Lagos zuwa Abuja sai abin farin ciki ya faru: matukin jirgin yana daga cikin dalibai dari da Kwankwason ya tura makarantar koyon tukin jiragen sama da ke kasar Jordan dan su koyi tukin jirgin sama.

Aminu Muhammad ya zama matukin jirgin saman Azman yau.
Sanatan Kano din ya bayyana farin cikin sa akan hakan.

Za a iya tuna cewa Kwankwason ya taba haduwa da wani matukin jirgin saman Azman din mai suna Hadi Sumaila a shekarar da ta wuce wanda shima matukin jirgin saman Azman din ne.

facebook din mu

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP