Abu ne me matukar wuya Ganduje ya sake cin zabe a Kano~ Tsohon mataimakin gwamna Hafiz Abubakar

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano mai da ya sauka kwanannan, Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa duba da irin yadda abubuwa ke gudana a siyasar jihar Kano, abu ne me matukar wuya ace Ganduje ya sake cin zabe a shekarar 2019.
Farfesa Hafiz yayi wannan bayani ne a lokacin da yake hira da jaridar The Punch.
Ya kara da cewa, PDP ce zata samu nasara a jihar a zabe me zuwa domin kuwa da yawa wadanda ke zagaye da gwamnan sun gaji da zama a APC saboda rashin adalcin da ake musu suna ta komawa PDP.
Yace 'yan majalisar jihar ma ba'a barsu a baya ba wajan canja shekar inda ya kara da cewa yana da yakinin tsohon gwamnan jihar, Sanata Kwankwaso ne zai samu tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a PDP a zaben 2019.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP