Posts

Showing posts from September, 2018

Yau Ce Ranar Zuciya Ta Duniya

________________ Zuciya wani sashin jikin ɗan'adam ne da ke harba jinin da ke ɗauke da iskar "Oxygen" da sinadaran abinci zuwa dukkan sassan jiki domin cigaban rayuwa. Haɗaɗɗiyar ƙungiyar lura da masu ciwon zuciya ta duniya ce ta ware ranar 29 ga watan Satumba na kowacce shekara domin gangamin wayar da kai dangane da kiyaye lafiyar zuciya. Binciken ƙwararru ya tabbatar da cewa motsa jiki ko atisaye na taka muhimmiyar rawa wajen: 1) Gina tsokar zuciya da share hanyoyin jini. 2) Rage hawan jini 3) Daidaita suga a cikin jini 4) Ƙone tararren kitse a cikin jini da sauran sasan jiki. 5) Daidaita sinadaran da ke angiza bugawar zuciya, da dai sauransu. Sai dai sau dawa za ka ji masana harkokin lafiya suna cewa a motsa jiki, ba tare da keɓe wanne irin motsa jiki ko atisaye ne ke da alfanu ga lafiyar jikin ba. Tuntuɓi likitan Fisiyo a yau domin neman shawarwari kan fara motsa jiki/atisaye domin dacewa da alfanun da aka ambata a sama. https://mobile.facebook.com/Physi

Zanga Zangar Ranar Ashura : Jami'an Tsaro Sun Bude Wuta Akan 'Yan Shi'a.

Image
Rahotanni daga birnin Zariyan Jihar Kaduna sun bayyana cewar rundunar 'yan Sandan jihar sun bude wuta gami da watsa barkonon tsohuwa akan dubban 'yan shi'a Maza da Mata wadanda ke gudanar da zanga zangar ranar ashura, domin nuna bakin ciki da alhinin su akan kisan da akayiwa jikan Annabi wato Sayyidina Hussain a Karbala. Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar, tun da sanyin asubahin ranar yau ce 'Yan Shi'an suka yi dafifi suka cika birnin na Zazzau sannan suka rurrufe hanyoyi suka hana jama 'a gudanar da harkokin su na yau da kullum, suna rera wakokin tsinuwa da La'antar wadanda suka aiwatar da kisan Sayyidina Hussain, hakanan kuma sun cigaba da La'antar wadanda suka kira a matsayin shugabanni masu koyi da azzaluman farko, inda suka rinka kiran sunan Buhari da Buratai da El Rufai suna tsine musu, lamarin da ya haifar da hatsaniya da kuma tarzoma a birnin.

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Image
Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000 Wani Mr. Sunday Ekpong ya kona yarinya 'yar shekara 13 da dutsen guga a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa akan batan kudin makocin su. Wanda ya yadda labarin a Facebook dinshi mai suna Efibre, ya cemakocin yaga kudin nasa da suka bata daga baya a inda ya ajiye su . Ranar Galata 5/9/2018 aka zargi karamar yarinyar da sace N3000 daga makocin su. Bayan bincike da barazana daga kawunta yarinyar ta dage akan cewa bata saci kudi ba. Kawunnata sai ya fara yi mata dukan rashin imani yana sa ta fito da kudi amma yarinyar ta dage akan bata saci kudi ba. Daganan ya cire mata kaya ya dauko dutsen guga mai zafi ya dinga danna mata a fuskar ta da nonon ta akan cewa ba zai daina ba har sai ta yarda ta saci kudin. Yarinyar ta amince da hakan dan ta samu saukin azabtarwar da yake mata. Abin bacin rai akan labarin shine makocin yaga kudin nasa a inda ya ajiyesu. Shi kuma kawun nata ya kaita asi

Hoton Messi 'Ya'yansa

Image
Hoton Messi 'Ya'yansa Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya sa hoton shi tare da 'ya'yan sa a Instagram dinshi yau.

Shekarau Ya Koma APC

Image
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP Zuwa APC. Dan tabbatar da wannan labari ga jaridar Daily Trust da safen nan, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u Sule, ya bayyana cewa tsohon gwaman ya yanke shawaran fita daga jam'iyyar ne bayan muhawara tsakaninsa da mabiyansa. Sule ya kara da cewa babu yadda zai yiwu su cigaba da kasancewa cikin PDP duba ga yadda shugabancin jam'iyyar ta kasa ya karkata kan Kwankwaso sabanin sauran shugabannin PDP a jihar.

Mutanen Da Hukumar Zabe Ta Yiwa Rajista Kawo Yanzu

Image
Sabon jerin adadin wadanda hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta yiwa rajista da suka cancanci kada kuri'a a zaben 2019. Kudu maso gabas Abia 1,481,191 Anambra 1,758,220 Enugu 1,301,185 Imo 1,611,715 Ebonyi 876,249 Adadi = 7,028,560 ------------------------------------------------------------------ *Kudu maso yamma:* *Lagos 6,247,845* *Ogun 1,869,326* *Osun 1,293,967* *Ondo 1,558,975* *Ekiti 750,753* *Oyo 2,577,490* *Adadi=14,298,356* ------------------------------------------------------------------ Kudu maso kudu: Edo 1,412;225 Delta 1,900,055 Bayelsa 472,389 Akwa Ibom 1,714,781 RIvers 2,419,057 C/Rivers 1,018,550 Adadi 8,937,057 ------------------------------------------------------------------ Arewa ta tsakiya: Benue 1,415,162 Kogi 1,215,405 Kwara 1,115,665 Nassarawa 1,224,206 Niger 721,478 Plateau 1,983,453 Adadi 7,675,369 ------------------------------------------------------------------ Arewa maso gabas: Adamawa 1,714,860 Bauchi 1,835,562