Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000
Wani Mr. Sunday Ekpong ya kona yarinya 'yar shekara 13 da dutsen guga a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa akan batan kudin makocin su.
Wanda ya yadda labarin a Facebook dinshi mai suna Efibre, ya cemakocin yaga kudin nasa da suka bata daga baya a inda ya ajiye su .
Ranar Galata 5/9/2018 aka zargi karamar yarinyar da sace N3000 daga makocin su. Bayan bincike da barazana daga kawunta yarinyar ta dage akan cewa bata saci kudi ba.
Kawunnata sai ya fara yi mata dukan rashin imani yana sa ta fito da kudi amma yarinyar ta dage akan bata saci kudi ba. Daganan ya cire mata kaya ya dauko dutsen guga mai zafi ya dinga danna mata a fuskar ta da nonon ta akan cewa ba zai daina ba har sai ta yarda ta saci kudin. Yarinyar ta amince da hakan dan ta samu saukin azabtarwar da yake mata.
Abin bacin rai akan labarin shine makocin yaga kudin nasa a inda ya ajiyesu. Shi kuma kawun nata ya kaita asibiti bayan raunukan da ya yi mata.
Labarin dai ya fashe ne bayan da washegarin abin makota suka ganta inda kuma ta kwashe labarin kaf ta gaya musu. Tuni dai kungiyoyin kare hakkin yara suka shiga cikin lamarin inda 'yan sanda suka kama kawunta nata, ita kuma tana samun kula ta musamman a asibiti.
Mai hakuri dai shi ke cin ribar rayuwa

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP