Zanga Zangar Ranar Ashura : Jami'an Tsaro Sun Bude Wuta Akan 'Yan Shi'a.


Rahotanni daga birnin Zariyan Jihar Kaduna sun bayyana cewar rundunar 'yan Sandan jihar sun bude wuta gami da watsa barkonon tsohuwa akan dubban 'yan shi'a Maza da Mata wadanda ke gudanar da zanga zangar ranar ashura, domin nuna bakin ciki da alhinin su akan kisan da akayiwa jikan Annabi wato Sayyidina Hussain a Karbala.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar, tun da sanyin asubahin ranar yau ce 'Yan Shi'an suka yi dafifi suka cika birnin na Zazzau sannan suka rurrufe hanyoyi suka hana jama 'a gudanar da harkokin su na yau da kullum, suna rera wakokin tsinuwa da La'antar wadanda suka aiwatar da kisan Sayyidina Hussain, hakanan kuma sun cigaba da La'antar wadanda suka kira a matsayin shugabanni masu koyi da azzaluman farko, inda suka rinka kiran sunan Buhari da Buratai da El Rufai suna tsine musu, lamarin da ya haifar da hatsaniya da kuma tarzoma a birnin.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Tsohon gwamnan jahar Gombe Abubakar Hashidu ya rasu

Cristiano Ronaldo ya hadu da abokan wasan sa na Juventus a karon farko

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Yunkurin Kawo Tarnaki A Ayyukan Ci Gaban Kasa Da Gwamnati Ke Yi Wa Talakawa

Tsohon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan, Ya Rasu