Tsohon gwamnan jahar Gombe Abubakar Hashidu ya rasu
Tsohon Gwamnan jihar Gombe, Abubakar Hashidu Ya Rasu
Shine gwamnan farar hula na farko a jihar Gombe, Abubakar Habu Hashidu ya rasu a yau Juma'a sakamakon rashin lafiya da ya jima yana fama da ita.
Ya rike mukamin Gwamnan Gombe ne daga 1999 zuwa 2003 a karkashin jam'iyyar ANPP. Sannan kuma ya yi ministan ruwa a zamanin mulkin soja karkashin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Comments