Buhari zai tafi jihar Lome dake kasar Togo gobe lahadi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi gobe zuwa Lome dake kasar Togo dan yin wadansu muhimman taruka guda biyu.
Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafofin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana haka yau asabar ga manema labarai.
Yace shugaban zai gana da yan Nigeria mazauna Togo da kuma ofishin jakadancin Nigeria a ran lahadin.
Ya kara da cewa shugaban zai halarci taron ECOWAS ran litinin.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP