A halin yanzu 'yan Nijeriya da dama na nuna wa mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo matukar so irin wanda ba kasafai 'yan siyasa ke samu ba, a kasar da ba a kallon galibin 'yan siyasa da kima sosai. Ana yaba wa mataimakin shugaban kasar saboda yadda ya dauki kwararan matakai ba tare da wata-wata ba yayin da ya rika wa Shugaba Buhari a matsayin mukaddashin shugaban Nijeriya, lokacin hutun shugaban na kwanaki goma a baya-bayan nan. Yanayin hobbasa da kazar-kazar din mutumin, mai shekaru 61 a duniya, ya sha bamban da yanayin jinkiri da jan-kafa na Shugaba Buhari, mai shekaru 75 a duniya, wanda wasu 'yan kasar ke wa lakabi da ''Baba Go-slow'', wato ''Baba Mai nawa.'' Manyan jami'an gwamnatin Najeriya dai na cewa duk wani mataki da mataimakin shugaban kasar ko kuma shi kansa Shugaba Buhari ya dauka, abu ne na gwmnati guda babu wani bambanci, kuma dukkanninsu sun zo ne da manufofi guda da zimmar aiki tare. Amma duk da haka w...
Comments