A jiya juma,a shararriyar yar fim din kanywood da nollywood wato Rahama Sadau ta bayyana farin cikin ta tare da haduwa da ta yi da yan uwanta shakikai.
Mai ba wa shugaban kasa shawara akan kafofin yada labarai, Femi Adesina, ya tabbatar da cewa Muhammad Buhari zai fara hutun aiki daga ranar Alhamis 03/08/2018. Shugaba Buhari zai yi hutun aikin ne a birnin London dake kasar England.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana komawar sa jam'iyyar PDP daga jam'iyyar APC. Tsohon shugaban majalisar tarayyar ya bayyana komawar sa ne a gaban dandazon magoya bayan sa a fadar gwamnatin jihar Sokoto. Gwamnan ya bayyana cewa a shirye yake don ganin Jam'iyyar PDP ta samu nasara a dukkanin matakan zabuka a shekarar 2019. Manyan yan siyasa na ta barin jam'iyyar APC
Kamfanin jaridar Daily trust, ya gano cewa an tsige shugaban majalisar ne saboda da zargin cin hanci da rashawa. Wani zargin kuma da su ke wa tsohon shugaban majalisar ya hadar da zuwa majalisa a makare. Sun kuma tuhume shi da rashin aiki tare da manyan ofisoshin majalisar wajen gudanar da majalisar. Wasu labaran na zuwa anjima.
Abubakar Duduwale da yayi tattaki daga garin yola zuwa birnin tarayya, Abuja dan murnar rantsar da Buhari a matsayin shugaban kasa ya samu ciwo a kafarsa. Duduwale dai yana Yola yanzu a cikin halin ha'ula'i kuma yana bukatar taimako.
Comments