Abu goma da ke janyo mutuwar barin jiki

  Mutuwar barin jiki na faruwa ne idan kwakwalwa ta gaza samun isashshen jini a dalilin fashewa ko toshewar magudanan jini da suke ba ta jini.
Duk bangaren kwakwalwa da ya kasa samun jini na tsawon minti daya yana mutuwa, sai bangaren jiki da wannan waje ke sarrafawa ya rasa aikinsa.

Abubuwa goma da za su iya janyo mutuwar barin jiki da suke sanadiyyar toshewa ko fashewar mesar da ta ke ba wa kwakwalwa jini sune:
1. Hawan jini.  Shi yafi komai yawan janyo mutuwar barin jiki. Alamun hauhawar jinin tana farawa daga 140/90mmHg.

2.  Taba sigari.  Hayakin sigari yana kara kaurin jini, yana kara gudun jini sannan kuma yana sa magudanan jini suyi tauri

3.  Ciwon zuciya.  Zuciya tana iya samun tawaya tun a cikin uwa ko a yayin tsufa ko ma kitse ya toshe manyan hanyoyin jinin.

4.  Ciwon sikari.  Akasarin masu wannan ciwon suna da hawan jini. Yawan sikarin a cikin jini na janyo lalacewar magudanan jinin.

5.  Kiba da te'ba.  Kiba tana da alaka da yawan kitse a cikin jiki, wannan kitsen na tausa muhimman sassan jiki kamar su zuciya da magudanan jini ya hanasu gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

6.  Magunguna. Magunguna da ake amfani da su kamar na tsinka jini ko na hana daukar jiki ka iya janyo wannan cuta idan ba a yi takatsantsan ba.

7.  Shekarau haihuwa. Wadanda su ka haura shekara 55 sun fi hatsarin kamuwa da cuta akan yan kasa da hawan

8.  Iyali.  Wannan cutar ana gadon ta kuma tana bin dangi kamar yadda bincike ya tabbatar.

9.  Jinsi. Kowa na iya samu amma tafi yiwa mata illa a yayin da ta kamasu a tsufan su.

10.  Kabila.  An fi samun cutar a cikin bakake, gabas ta tsakiya da yankin Asia.

Zama waje daya da rashin motsa jiki na tsawon lokaci na yiwa magudan jini illa sosai! Sai a kiyaye.
Sa email din ka a nan dan samun sababbin labaranmu kai tsaye.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019