Alamomi 16 da za su tabbatar wa namiji mace tana sonsa
1. KALLO: Mata suna aika sakonni da yawa ta hanyar kallo, kamar So, raini, tsoro, ba ruwana dakai da sauransu, kuma kowane ba sai an fassarawa mutum ba da ya gani yasan me ake nufi
2. KULAWA: Wannan na nufin ta nuna ta damu dashi a kowanne lokaci, ta hanyar kokarin jin halin da yake, lafiyarsa da kuma al'amuransa. Ko yana kusa da ita ko kuma nesa da ita. Idan abun murna ya sameshi ta tayashi idan na jaje ya sameshi ta jajanta masa. Ba shakka wannan yana nuna soyayya.
3. BIYAYYA: Mace ta rinka girmama namiji, abokansa da 'yan'uwansa a duk lokacin da zata mu'amalance shi ko su, a gaisuwa ne, a magana ce, a rubutaccen sako ne duk wadannan yana bukatar yaga ladabi acikinsu kada ta rinka yi masa tsiwa da rashin kunya da sauran dabi'u da zasu nunawa mutum ba a dauke shi abakin komai ba.
4. HAKURI: Babban abinda yafi bada wahala a mu'amala kuma a kafi jarraba mutum akai shine hakuri, ya zamanto namiji ya gamsu da hakurin mace ta kowace hanya kar ta rinka yi masa koke-koke, ko ta zama mai rainuwa, duk abinda ya bata tayi hakuri dashi kar tace bai kai kaza ba ko kuma bai kai na wance ba, idan sabani ya shiga kada tayi jayayya dashi idan kuma taga yayi fushi ta rarrasheshi tace yayi hakuri.
5. UZURI: Anan ana nufin mace ta zama mai karbar hanzarinsa duk lokacin da wani abu ya faru, misali, ta buga masa waya bai dauka ba ko ta tura masa sako bai bata amsa ba, kada tayi fushi tace shikenan tunda abin wulakancine bazan sake kira ba, ta daure ta cigaba da neman jin me yake faruwa kafin ta yanke hukunci, domin akwai dalilai da yawa dake iya sa hakan ta kasance kamar rashin lafiya, faduwar wayar da sauransu. Idan kuma ya kirata daga baya shima ta dauka cikin farin ciki ba da fushi ba, har taji dalilinsa, kuma koda ya kawo mata hujja ta karya kuma ta gane to tayi dariya acikin ranta kawai kada ta nuna masa ta harbo jirginsa.
6. TAUSAYI: Mace ta zama mai tausayawa namiji don shi namiji har kirari ake masa da cewa "Zakara mai neman suna, bada kwaya kaci tsakuwa" saboda haka ta kalli wane shi da idan basira kamin ta koro masa wasu bukatun, kada tasa ya rinka jin tsoron zuwa gurinta, ko kuma da yaga kiranta gabansa ya fadi don yasan matsala za'a karanta masa. Wani kuma ba dora masa bukatar za a yi ba a'a, shi zai dorawa kansa amma zai kokarin yin abinda yafi karfinsa don kar ace ya gaza ko kuma ace kai wane BA dama! Da sauran dalilai, to shi wannan birki za tai ta taka masa.
7. TATTALI: Duk abinda namiji ya yiwa mace tayi kokarin tattala wannan abun, kada ta zama mai barna ko almubazziranci don gadarar ko yanzu nace ya sake yimin zaiyi.
8. SHAWARA: Idan namiji yaga a mafi yawancin lokaci mace takan shawarceshi acikin wasu lamuranta na rayuwa wanda shi yasan ba lallai bane ta sanar dashi kuma yasan ba wani abinsa take jira ko sa rai ba kuma bashi kadai ya iya bada shawaraba, to wannan yana bashi sakon cewa ana tare dashi.
9. ALFAHARI: Wato mace ta nunawa namiji shi wani ne a gurinta, a gaban kowa, ko an tambayeta ko ba a tambayeta ba, ba idan anji tana waya dashi a tambayeta wane tace 'wani ne yake ta damuna nace ya daina kirana amma yaki' ko kuma tace 'saurayin kawatane' muke gaisawa. A'a tace ni da (Baraune) ta fadi sunansa.
10. KYAUTATA ZATO: Mace ta yiwa namiji zato na alkhairi kada ta munana masa zato ko tai ta kokarin gano wadansu kura-kurensa koda kuwa yanayi, matukar ya sirrintasu har sai idan yaqini ya zo mata.
11. YAFIYA: Babu yadda za'ayi a gina mu'amalar da sabani bazai shigo ba, don haka mace ta zama me afuwa ga namiji a duk lokacin da sabani ya yazo, kada ta dage akan lallai ita tana da hakki, koda tana dashi din ta yafe wannan zai kara mata daraja ko ba a sannan ba ko zuwa gabane, kuma kada a yafe a baki amma a zuciya.... Ko kuma ranar da wani sabanin yazo ace dama rannan ma ... Kada tayi haka.
12. KYAUTATAWA: Ya zamana duk lokacin da zaije wajenta to ta kyautata masa kada yaji cewa bata mutuntashi ba.
13. KARIYA: Shine mace ta zama me kare namiji daga dukkanin abinda zai cutar dashi ko kuma mutuncinsa, ya zamana wani ko wata bazai ci zarafinsa ba matukar tana wurin koda kuwa danuwantane.
14. TSAFTA: Ya zamana duk lokacin da namiji zai hadu da mace to ya ganta kamar sannan za'a kaita gidan miji .......
15. NUTSUWA: Mace ta zama mai sa namiji farin ciki a koda yaushe, har ya zamto koda an bata masa rai a wani gurin ko kuma wasu alamuran sun sha masa kai zai iya zuwa gurinta ko kuma kiranta suyi maganar don yasan zata rarrasheshi har ya sami nutsuwa da kwanciyar hankali.
16. GASKIYA: mace ta kasance mai bayyanar da gaskiyarta ga namiji a duk abinda za suyi, kada karya, cutarwa, rashin gaskiya ya fito a gurinta komai kankantarsa.
Source: isyaku.com

Comments