Buhari ya bukaci magoya bayansa da su dakatar da yakin neman zaben sa a halin yanzu
A jiya asabar Shugaba Muhammad Buhari ya roki magoya bayan sa na kasa gaba daya da su dakatar da yakin neman zaben sa da su ka fara. Ya yi wannan furucin ne ta bakin mataimakin sa a kan yada labarai wato Femi Adesina inda ya kara da cewa hukumar zabe tana da jadawalin ta na harkokin siyasa, dan haka suyi hakuri lokacin ya yi.
Buhari ya ce ya yaba da kaunar da suke nuna masa kuma zai tanadar da aiyukan ci gaba da za su yi amfani da su wajen nuna nasarar da gwamnati ta yi a kan ci gaban kasa.
Buhari ya ce ya yaba da kaunar da suke nuna masa kuma zai tanadar da aiyukan ci gaba da za su yi amfani da su wajen nuna nasarar da gwamnati ta yi a kan ci gaban kasa.
Comments