Shekarau Ya Koma APC
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP Zuwa APC.
Dan tabbatar da wannan labari ga jaridar Daily Trust da safen nan, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u Sule, ya bayyana cewa
tsohon gwaman ya yanke shawaran fita daga jam'iyyar ne bayan muhawara tsakaninsa da mabiyansa.
Sule ya kara da cewa babu yadda zai yiwu su cigaba da kasancewa cikin PDP duba ga yadda shugabancin jam'iyyar ta kasa ya karkata kan Kwankwaso sabanin sauran shugabannin PDP a jihar.
Comments