Za a yi babbar sallah ran talata a Kano

Babban kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ranar Talata 21 ga wannan watan ne ranar babbar Sallah a Najeriya.
Kwamitin ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana dalilinsa na yin haka:
"A kan batun cewa Saudiyya ta bayyana ranar Dhl Hijjah da ta bambanta da wanda muka riga muka bayyana, kwamitin ganin wata ya tuntubi babban kwamitin Fatawa na kasa a shekarun baya, kuma an fitar da wata Fatawa mai cewa ya kamata mu rika bin hukuncin ganin watan da kasar Saudiyya ta yanke na Dhul Hijjah saboda muhimmancin hawan Arafat."
Wannan sanarwar ta ci karo da sanarwar farko da kwamitin ya fitar.
Sanarwar kwamitin ta cigaba da cewa, "A kan haka ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, bayan ya tuntubi kwamitin Fatawa da kwamitin ganin wata da sauran malaman addini har da sarakunan gargajiya, ya bayyana Lahadi 12 ga watan Agusta 2018 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah 1439H."

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019