Yaro Dan Shekara 14 Da Ya Fito Takarar Gwamna A Amerika
Yaro mai suna Ethan Sonneborn dan shekara 14 da bai kai shekarun kada kuri'a ba ko jan mota da kansa ya fito takarar gwamna a garin Vermont da ke Amerika.
Yaron da ya ke neman jam'iyyar democrat ta tsayar da shi takarar gwamnan zai yi hakan ne saboda dokar yankin na su ba ta kayyade shekarun da mutum zai kai kafin ya tsaya takarar gwamnan ba.
Sharadin kawai shine kowanne dan takara ya zama mazaunin garin na akalla shekara 4, shi kuma Soneburn shekarun Sa sha hudu a garin.
Za su dai yi zaben fidda dan takara ranar talata shi da wasu manya guda uku.
Comments