Mata sun fi maza shaye-shaye a Kano da katsina - wata kungiya ta fada

Kungiyar mata ta arewa ta janyo hankalin gwamnatin tarayya akan kara yawaitar mata masu ta'ammuli da miyagun kwayoyi a garin Kano da Katsina, tana nuna cewa mata sun fi maza shan miyagun kwayoyi a bangarorin.

Kungiyar a wani taro a Abuja ta ce, binciken ta ya nuna cewa mata da yawa yanzu suna amfani da miyagun kwayoyi saboda "bacin rai, miyagun kawaye da kuma rashin ilimi".

Shugabar kungiyar matan arewan, Mrs. Aisha Hussain, ta ce za a shawo kan shaye-shayen miyagun kwayoyi da mata suke yi ne idan gwamnati da sauran jama'a suka tashi tsaye wajen wayar da kan jama'a.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019