Wani ma'aikacin access bank ya sace naira miliyan sha uku da dubu dari shida na kwastoman bankin

Wani ma'aikacin banki dan shekara ashirin da tara,Kolawale Agboola, ya bayyana ran juma'a a kotun chief magistrate akan zargin satar kudi miliyan goma sha uku da dubu dari shida, na kwastomomi biyu da ke hulda da bankin access.
Mai gabatar da karar, Ajibode, ya ce Wanda ake tuhuma din ya cire kudi daga asusun kwastoman da ba a bayyana ba ta hangar amfani da takaddun bogi dan ya sakaya aikin damfarar tasa.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Ya Bar APC Zuwa PDP