Allah Karawa Najeriya Albarka - Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, yayi wa iyalin sa da kasa Najeriya addu'ar neman albarka, inda ya rubuta a shafin sa na fesbuk kamar haka, " Allah ya ci gaba da karo albarkoki akan mu, iyalanmu da kasarmu a wannan rana ta Arafah. La ilaha ilallah, wahdahu la sharikallah, lahul mulk walahul hamd wa huwa ala kuli shayin Qadeer."
Comments