Amarya ta watsawa uwargidan ta tafasashshiyar miyar kuka a Jihar Jigawa
Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba ta na dakin girki sai uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan sai amaryar ta fara mayar mata da magana.
Daga nan sai cacar baki ta kaure, ba tare da bata lokaci ba ne kuma amaryar ta dauki tukunyar miya tana tafarfasa ta watsawa uwargidan da danta a jikinsu.
Bayan ta watsa musu miyar ne, sai amaryar kuma ta fara ihu na neman a kawo musu agaji.
Mai magana da yawun yan sandan ya ce uwargidan da danta yanzu haka suna babban asibitin Dutse suna karbar magani, kuma duk jikinsu ya sabule musamman ma yaron.
Kwamshinan yan sandan jihar, CP Bala, ya bayar da umarnin a kai amaryar da ta aikata lamarin sashen binciken kwakwaf domin gudanar da bincike da kuma yi mata hukuncin da ya dace.
Majiyar mu ta BBC ta yi kokokarin jin ta bakin mijin matan wato Malam Hamza, amma wayarsa a rufe.

Comments