An Kirkiro Sabon Manhajar Da Za Ta Rage Yawan Batan Alhazai

Hukumar da ke kula da gudanar da aikin hajji ta najeriya, NAHCON, ta bayyana cewa ta kirkiro wata sabuwar manhaja da za ta rage yawan batan alhazai a lokacin aikin hajji.
Hukumar ta ce fasahar na'ura mai kwakwalwar  ta GPS za ta dinga nuna wa alhazai taswirar wajen da suke da kuma inda suke nema. Manhajar tana dauke da shafin yanar gizo kuma an sanya ta a dukkan shemomin jihohin kasar ta yadda za a iya latsa duk wacce mutum ke nema daga ko ina, kamar filin Arfa da Muzdalifa da wajen jifa.
Kuma nan take za ta nuna wa mutum taswirar inda zai bi ta manhajar Google map.
Sai dai manhajar za ta dinga aiki ne kawai a wayoyin komai da ruwanka. Hukumar ta NAHCON ta ce ta kuma samar da wasu lambobin waya da alhazai za su iya kira ba dare ba rana domin neman taimako.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019