Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019

Yayin da shekarar zabe ta 2019 ke ta kara matsowa, masana harkokin siyasa da ma masu fashin baki akan al’amurra na ganin cewa har yanzu fa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke kan gaba wajen farin jini a al’ummar kasar.
Kamar yadda suka bayyana za’a iya ganewa idan aka yi duba na tsanaki a tsakanin kafatanin jahohin Najeriya aka kuma dora su akan sikelin wadanda zai iya lashewa da kuma faduwa a zaben mai zuwa.
Duk da dai har yanzu jam’iyyar adawa ta PDP bata fitar da nata dan takarar ba, amma dai ana hasashen cewa shugaba Buhari zai iya lashe akalla jahohi 21 a zaben mai zuwa.
Idan kuma aka hada da babban birnin tarayya, to a iya cewa ma jahohi 22.
Ga dai su kamar haka:
1. Adamawa
2. Bauchi.
3. Borno
4. Ekiti
5. Gombe
6. Jigawa
7. Kaduna
8. Kano
9. Katsina
10. Kebbi
11. Kogi
12. Lagos
13. Nasarawa
14. Niger
15. Ogun
16. Ondo
17. Osun
18. Oyo
19. Sokoto
20. Taraba
21. Zamfara
22. Sai kuma babban birnin tarayya Abuja.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano