Illar Shan Magunguna Barkatai
Abin da ya kamata ka sani dangane da shan magungunan ciwon jiki barkatai. __________________ Ɗabi'ar shan magungunan ciwon jiki da gaɓɓai ɗabi'a ce da ta zama ruwan dare, sai dai jinsin magungunan rage ciwo, raɗaɗi, ko zafin jiki da ake cewa NSAIDs (Nonsteroidal Anti-inflammatory Drugs) ba sune mafita ga masu fama da ciwon jiki ba, kamar masu fama da ciwon baya, ciwon wuya, ciwon gwiwa da sauransu. Domin irin waɗannan ciwuka suna faruwa ne sakamakon saɓanin zaman ƙashi, jijiya da tsoka a jiki. Saboda haka ciwon jiki ko ciwon wata gaɓa na faruwa ne a matsayin alama ko gargaɗi cewa an sami saɓani tsakanin tsoka, ƙashi ko jijiya. Wannan ne yasa ko mutum ya sha maganin ciwon jiki da zarar ƙarfin maganin ya ƙare a cikin jini to wannan ciwo zai dawo har sai an sake shan wani maganin kuma. A taƙaice jinsin waɗannan magunguna ba sune haƙiƙanin matsalar ciwo ba dangane da ciwukan jiki da suke da asali daga jijiya, ƙashi da tsoka. Haka nan waɗannan magunguna suna a matsayin shamaki ...