Posts

Showing posts from 2018

Ado Gwanja Ya Angwance

Image
Fitaccen jarumin nan da kan fito a fina-finan Hausa na masana'antar Kanyywood kuma mawaki da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamanin, Adamu Isa wanda aka fi sani da Gwanja ya angwance a yau asabar, 13 ga watan Oktoba 2018. Mawaki Ado Gwanja dai ya auri masoyiyar sa ce mai suna Maimuna Kabir Hassan kuma an daura auren ne a garin Kano a yau asabar da misalin karfe 11 na safe a kan titin zuwa gidan Zoo. Ado Gwanja yanzu yafi shahara ne a harkokin wakokin bukukuwa da wadanda suka shafi mata duk kuwa da cewa a wasu lokuttan yakan yi wakokin fina-finai da kuma na siyasa.

Yau Ce Ranar Zuciya Ta Duniya

________________ Zuciya wani sashin jikin ɗan'adam ne da ke harba jinin da ke ɗauke da iskar "Oxygen" da sinadaran abinci zuwa dukkan sassan jiki domin cigaban rayuwa. Haɗaɗɗiyar ƙungiyar lura da masu ciwon zuciya ta duniya ce ta ware ranar 29 ga watan Satumba na kowacce shekara domin gangamin wayar da kai dangane da kiyaye lafiyar zuciya. Binciken ƙwararru ya tabbatar da cewa motsa jiki ko atisaye na taka muhimmiyar rawa wajen: 1) Gina tsokar zuciya da share hanyoyin jini. 2) Rage hawan jini 3) Daidaita suga a cikin jini 4) Ƙone tararren kitse a cikin jini da sauran sasan jiki. 5) Daidaita sinadaran da ke angiza bugawar zuciya, da dai sauransu. Sai dai sau dawa za ka ji masana harkokin lafiya suna cewa a motsa jiki, ba tare da keɓe wanne irin motsa jiki ko atisaye ne ke da alfanu ga lafiyar jikin ba. Tuntuɓi likitan Fisiyo a yau domin neman shawarwari kan fara motsa jiki/atisaye domin dacewa da alfanun da aka ambata a sama. https://mobile.facebook.com/Physi...

Zanga Zangar Ranar Ashura : Jami'an Tsaro Sun Bude Wuta Akan 'Yan Shi'a.

Image
Rahotanni daga birnin Zariyan Jihar Kaduna sun bayyana cewar rundunar 'yan Sandan jihar sun bude wuta gami da watsa barkonon tsohuwa akan dubban 'yan shi'a Maza da Mata wadanda ke gudanar da zanga zangar ranar ashura, domin nuna bakin ciki da alhinin su akan kisan da akayiwa jikan Annabi wato Sayyidina Hussain a Karbala. Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar, tun da sanyin asubahin ranar yau ce 'Yan Shi'an suka yi dafifi suka cika birnin na Zazzau sannan suka rurrufe hanyoyi suka hana jama 'a gudanar da harkokin su na yau da kullum, suna rera wakokin tsinuwa da La'antar wadanda suka aiwatar da kisan Sayyidina Hussain, hakanan kuma sun cigaba da La'antar wadanda suka kira a matsayin shugabanni masu koyi da azzaluman farko, inda suka rinka kiran sunan Buhari da Buratai da El Rufai suna tsine musu, lamarin da ya haifar da hatsaniya da kuma tarzoma a birnin.

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Image
Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000 Wani Mr. Sunday Ekpong ya kona yarinya 'yar shekara 13 da dutsen guga a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa akan batan kudin makocin su. Wanda ya yadda labarin a Facebook dinshi mai suna Efibre, ya cemakocin yaga kudin nasa da suka bata daga baya a inda ya ajiye su . Ranar Galata 5/9/2018 aka zargi karamar yarinyar da sace N3000 daga makocin su. Bayan bincike da barazana daga kawunta yarinyar ta dage akan cewa bata saci kudi ba. Kawunnata sai ya fara yi mata dukan rashin imani yana sa ta fito da kudi amma yarinyar ta dage akan bata saci kudi ba. Daganan ya cire mata kaya ya dauko dutsen guga mai zafi ya dinga danna mata a fuskar ta da nonon ta akan cewa ba zai daina ba har sai ta yarda ta saci kudin. Yarinyar ta amince da hakan dan ta samu saukin azabtarwar da yake mata. Abin bacin rai akan labarin shine makocin yaga kudin nasa a inda ya ajiyesu. Shi kuma kawun nata ya kaita asi...

Hoton Messi 'Ya'yansa

Image
Hoton Messi 'Ya'yansa Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya sa hoton shi tare da 'ya'yan sa a Instagram dinshi yau.

Shekarau Ya Koma APC

Image
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP Zuwa APC. Dan tabbatar da wannan labari ga jaridar Daily Trust da safen nan, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u Sule, ya bayyana cewa tsohon gwaman ya yanke shawaran fita daga jam'iyyar ne bayan muhawara tsakaninsa da mabiyansa. Sule ya kara da cewa babu yadda zai yiwu su cigaba da kasancewa cikin PDP duba ga yadda shugabancin jam'iyyar ta kasa ya karkata kan Kwankwaso sabanin sauran shugabannin PDP a jihar.

Mutanen Da Hukumar Zabe Ta Yiwa Rajista Kawo Yanzu

Image
Sabon jerin adadin wadanda hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta yiwa rajista da suka cancanci kada kuri'a a zaben 2019. Kudu maso gabas Abia 1,481,191 Anambra 1,758,220 Enugu 1,301,185 Imo 1,611,715 Ebonyi 876,249 Adadi = 7,028,560 ------------------------------------------------------------------ *Kudu maso yamma:* *Lagos 6,247,845* *Ogun 1,869,326* *Osun 1,293,967* *Ondo 1,558,975* *Ekiti 750,753* *Oyo 2,577,490* *Adadi=14,298,356* ------------------------------------------------------------------ Kudu maso kudu: Edo 1,412;225 Delta 1,900,055 Bayelsa 472,389 Akwa Ibom 1,714,781 RIvers 2,419,057 C/Rivers 1,018,550 Adadi 8,937,057 ------------------------------------------------------------------ Arewa ta tsakiya: Benue 1,415,162 Kogi 1,215,405 Kwara 1,115,665 Nassarawa 1,224,206 Niger 721,478 Plateau 1,983,453 Adadi 7,675,369 ------------------------------------------------------------------ Arewa maso gabas: Adamawa 1,714,860 Bauchi 1,835,562 ...

Illar Shan Magunguna Barkatai

Abin da ya kamata ka sani dangane da shan magungunan ciwon jiki barkatai. __________________ Ɗabi'ar shan magungunan ciwon jiki da gaɓɓai ɗabi'a ce da ta zama ruwan dare, sai dai jinsin magungunan rage ciwo, raɗaɗi, ko zafin jiki da ake cewa NSAIDs (Nonsteroidal Anti-inflammatory Drugs) ba sune mafita ga masu fama da ciwon jiki ba, kamar masu fama da ciwon baya, ciwon wuya, ciwon gwiwa da sauransu. Domin irin waɗannan ciwuka suna faruwa ne sakamakon saɓanin zaman ƙashi, jijiya da tsoka a jiki. Saboda haka ciwon jiki ko ciwon wata gaɓa na faruwa ne a matsayin alama ko gargaɗi cewa an sami saɓani tsakanin tsoka, ƙashi ko jijiya. Wannan ne yasa ko mutum ya sha maganin ciwon jiki da zarar ƙarfin maganin ya ƙare a cikin jini to wannan ciwo zai dawo har sai an sake shan wani maganin kuma. A taƙaice jinsin waɗannan magunguna ba sune haƙiƙanin matsalar ciwo ba dangane da ciwukan jiki da suke da asali daga jijiya, ƙashi da tsoka. Haka nan waɗannan magunguna suna a matsayin shamaki ...

UEFA Ta Fitar Jadawali. Modric Ya Yi Fice

Image
Hukumar da ke gudanar da wasan zakarun turai, UEFA, ta fitar da jadawalin rukunan wasan da za a yi (champion league) a kaka mai zuwa. Hukumar ta kuma zabi dan kasar Croatia dake buga wa Real Madrid wasa, Luka Modric', a matsayin dan kwallon da yayi fice. Cristiano Ronaldo ne ke biye masa sai kuma Mohammed Salah a matsayin na uku Group A Atlético Madrid, Dortmund, Monaco, Club Brugge Group B Barcelona, Tottenham, PSV, Inter Milan Group C PSG, Napoli, Liverpool, Crvena zvezda Group D Lokomotiv Moskva, Porto, Schalke, Galatasaray Group E Bayern Munich, Benfica, Ajax, AEK Anthens Group F Man. City, Shakhtar Donetsk, Lyon, Hoffenheim Group G Real Madrid, Roma, CSKA Moskva, Plzeň Group H Juventus, Man Utd, Valencia, Young Boys

Saraki Zai Tsaya Takara

Image
Shugaban majalisar dattijai na Najeriya, Dr. Bukola Saraki, Ya bayyana aniyarsa ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2019, Inda Ya sha Alwashin Kai Najeriya ga nasara Shugaban majalisar na Dattawan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, a yayin taron tattaunawa da matasa da aka gudanar a otal din Sheraton da ke Abuja.

Yan Takarar Shugabancin Kasa 42

Image
      Adadin wadanda suka bayyana aniyar su ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019 ya kai 42 zuwa yanzu.  Ga sunayen su: 1. Kingsley Moghalu 2. Sule Lamido 3. Donald Duke 4. Kabiru Tanimu Turaki 5. Ahmed Mohammed Makarfi 6. Ibrahim Dankwambo 7. Muhammadu Buhari 8. Fela Durotoye 9. Funmilayo Adesanya-Davies 10. Remi Sonaiya 11. Thomas-Wilson Ikubese 12. Omoyele Sowore 13. Enyinnaya Nnaemeka Nwosu 14. Ahmed Buhari 15. Adesanya Fegbenro-Bryon 16. Charles Udeogaranya 17. Mathias Tsado 18. Eniola Ojajuni 19. Olu James Omosule 20. Tope Fasua- Anrp 21. Elishama Rosemary Ideh 23. Usman Ibrahim Alhaji 24. Datti Baba Ahmed 25. Adamu Garba 26. Chris Emejuru 27. Oluwaseyitan Lawrence Aletile 28. Omike Chikeluba Lewis 29. Ibrahim Ladaja 30. Omololu Omotosho 31. Fidelis Akhalomen Lawrence Ekoh 32. Alhaji Atiku Abubakar 33. Ibrahim Shekarau 34. Professor Iyorwuese Hagher 35. Chike Ukaegbu 36. Attahiru Bafarawa 37. Rabiu Musa Kwan...

Kwankwaso Ya Kaddamar Da Takarar Sa

Image
Sanatan Kano ta tsakiya, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kaddamar da takarar sa ta neman shugaban kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP. Tsohon gwamnan Kano din ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar ga dubban magoya bayan sa da akasarin su ke sanye da jar hula infa akayi taron a Cida Hotel da ke Jabi and garin Abuja.

Kwallon Da Ronaldo Ya Ci Juventus Ta Zo Ta Daya A Nahiyar Turai

Image
Hukumar da ke gudanar da kwallo a nahiyar turai, UEFA, ta zabi kwallo ta biyu da Cristiano Ronaldo ya ci Juventus a yayin karawar su da Real Madrid a kakar wasannin da ta gabata, a matsayi na daya. Dan Portugal din dai ya sami kyautar bayan cin watsiya da yayi a yayin wasan  da saida hakan ya burge magoya bayan Juventus din da har suka tashi tsaye suka jinjina masa akan bajintar da yayi.

Birtaniya Ta Dawowa Da Najeriya £70m

Birtaniya ta dawowa da Najeriya £70m, ta yi alkawarin dawo da kari anan gaba Gabanin zuwan Firam Ministan Birtaniya nan Najeriya, gwamnatin kasar ta dawowa da Najeriya da wasu makudan kudade da wani ma’aikacin gwamnatin Najeriya ya kai kasar. Kasar Birtaniya ta dawowa Najeriya da makudan kudi £70m da aka kwato daga hannun wani barawon gwamnati da ya sace kuma wata kotun Italiya ta kama shi. Jakadan Birtaniya zuwa Najeriya, Mr Paul Arkwright, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai a birnin tarayya Abuja. Yace:“Akwai wata karar kotun Italiya da wani mutum, Wani kashin kudin na ajiye kasar Birtaniya kuma an maido da kudin Najeriya kwanan nan. Saboda hakane aka dawo da Fam milyan 70." Amma jakadan Mr Paul Arkwright,ya ki bayyana sunan dan Najeriyan da ya kai kudin Najeriya wajen. Ya ce dai za’a dawo da karin kudi inda ya jaddada cewa kasarsa na aiki da gwamnatin Najeriya domin kara saurin gudun yadda za’a dawo da su.

Yunkurin Kawo Tarnaki A Ayyukan Ci Gaban Kasa Da Gwamnati Ke Yi Wa Talakawa

Image
Rundunar 'yan sanda ta kama wasu mutane uku daga cikin mutanen da suke lalata layin dogon da gwamnatin tarayya ke kokarin farfado da shi domin sada jihohin kasar nan cikin sauki. An kama wadannan mutane ne a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, izuwa yanzu jami'an 'yan sanda suna ci gaba da bincike akan wadannan mutane domin tatsar bayanai akan wannan aika-aika da suke tafkawa.

Roman Abramovich Ya Sa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea A Kasuwa

Image
Jaridar Sunday times sun ruwaito cewa mamallakin kungiyar kwallon kafa ta chelsea, Roman Abramovich, ya hayo wani banki dake New York mai suna 'Raine Group' dan yayi masa dillanci akan shirin sa na sayar da kulob din. Bankin dai an ce yayi ma kulob din kiyasin kudi £2billion ( Naira tiriliyan 840 ). Abramovich ya sayi Chelsea din a 2003 akan kudi £140 million ( Naira biliyan 58.8 ). Sune kulob din London na farko da ya dau kofin zakarun turai a shekarar 2012.

Kada Ku Sassauta Wa 'Yan Ta'adda - Sakon Buhari Ga Sojoji

Image
      Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bukaci sojojin kasar da kada su sasauta wa 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma masu satar dabbobi. Shugaban ya bayyana haka ne a yau Asabar a filin jirgin saman Katsina lokacin da yake ganawa da sojojin gabanin komawarsa Abuja bayan ya yi hutun babbar sallah a mahaifarsa dake Daura. Sojojin na cikin rundunar Operations Sharan Daji da Diran Mikiya wadanda aka tura jihar Zamfara da makwabtan jihohi domin magance matsalar barayin mutane da shanu da kuma 'yan fashi da makami.

Hoton Attajiran Najeriya Da Ya Za Ja Hankalin Jankalin Mutane

Image
Wasu daga cikin yan Najeriya na ta cece-kuce akan akan wannan hoton fake kunshe da manyan attajiran kasar a yayin da suke gudanar bukukuwan sallar su cikin saukin kai. Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabi'u ne ya sauke su. Wanda ya fi kudi a afirka, Aliko Dangote, Femi Otedola, Sam Iwuajoku da Richie Shittu tare da mai masaukin su sun yi hoto 'ba tare da kayan kwalan da makwalashe akan teburin ba' shi ya ja yan Sa ido me surutai akan hakan.

Wani Mahajjaci Ya Fado Daga Rufin Masallacin

Image
Wani Mahajjaci Ya Fado Daga Rufin Masallacin Harami Majiyar mu ta rariya ta ruwaito cewa "hukumomi a Saudiyya sun tabbatar da yau Juma'a misalin karfe 8:10 na safe wani mutum ya fado daga rufin dake Masallacin Harami zuwa kasa wajen da ake Dawafi abinda ya yi sanadiyyar mutuwar sa nan take tare kuma da raunata wasu mutane biyu."

Kwankwaso Ya Hadu Da Jonathan

Image
Mai girma tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, a gidan sa da ke Maitama, Abuja. Akwai yiwuwar cewa dai ziyarar tana da alaka da aniyar tsohon ministan na jam'iyyar PDP ta tsaida shi a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa a zabe mai gabatowa.

Ina San 'Yan Najeriya Su Zabeni Dan Nayi Aiki Ba Dan Tafiyar kafa Ba - Atiku

Image
 Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa shi yana yawan motsa jiki gami da sassarfa na sama da mil daya, amma yin hakan ba wani abu ne na bajinta da zai nemi 'yan Najeriya su zabe shi a kan hakan ba.  Turakin Adamawan ya kara da cewa yana so jam'iyyar sa -PDP da yan Najeriya su zabe shi dan aikin sa ba dan tafiyar kafa ba. Ya kara da cewa zai yi aiki dan ya kirkiri ayyuka, ba kuma zai yi tafiyar kafa dan ya kirkiri abin da ba hakan ba ne.

LAIFIN KWANKWASO 'DAYA !!!

Image
   Ra'ayin A lhaji Sharif Hifzullah Laifin Kwankwaso daya dai shi ne ya nemi kujerar Buhari. Maganar zargin sata kuwa, idan ka cire Buharin, babu wanda ba'a zargin sata akansa har da muqarraban Buharin. Amma idan ka natsu da kyau, ka dubi yadda Kwankwaso ya tura 'ya'yan talakawa da ya tura karatu, wadanda tuni suka fita qangin talauci da zaman banza, zaka iya cewa tun daga Sardauna, ba'a qara samun mai kishin Arewa ba kamar Kwankwaso. A lokacin da aka kama masu farauta daga Jigawa a garin Imo, ana zarginsu da zama 'yan Boko Haram, a 2014, Kwankwason dai ya kai masu dauki. Wataqila da har yanzu suna can garqame ko kuma ankashe su. Haka ya yi tattaki har zuwa Ile-Ife inda ake kashe Hausawa a garin. Ya kuma je Mile 12 a lokacin da aka kashe Hausawa. Zuwansa Ile Ife ya sanya duk wadanda ake zargi akan rikicin aka mayar da su a Abuja domin yi masu shari'a. A yanzu, Yarabawa sun fi kowa amfana da wannan gwamnatin ta Buhari a fannin ayyukan titi, hanyoyin jirg...

Buhari Ya Taka Kafa Daga Masallacin Idi Zuwa Gida

Image
Shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari, yayi sallar idi a garin Daura da ke jihar Katsina a yau inda ya taka da kafa tsawon mita 800 tun daga masallacin idin garin zuwa gidan sa a Daura. Mutanen da dama su fito dan tarar shugaban kasar inda suka dinga ihun 'said baba!'.  Muhammad Buhari na yanka ragon layyar sa a gidan sa na Daura bayan ya dawo daga masallacin idi.

Buhari Ya Isa Daura Dan Gudanar Da Bikin Sallah

Image
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya baro fadar hugaban kasa da ke Abuja zuwa garin Daura a Katsina, dan gudanar da bikin sallar layya. Ya sauka a tashar jiragen sama ta Umaru Musa Yar'adua yau litinin da yamma kafin daga bisani ya zarce garin Daura.

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar Da Ta Yiwa Dalibai A Watan July

Image
Hukumar da ke shiryawa daliban sakandare Jarrabawar satifiket (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar da ta yi wa dalibai a watan June/July. Daga cikin jimillar dalibai 1,041,536 da suka rubuta Jarrabawar guda 742,455 ne kawai su ka samu akalla kiredit 5 da suka kunshi turanci da lissafi. Hukumar ta kuma tabbatar da kama dalibai guda 20,181 da magudin Jarrabawa.

Buhari ya gana da shuwagabannin tsaro yau litinin

Image
A yau litinin ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya jagoranci zaman ganawa da shuwagabannin rundunonin tsaro na kasa a fadarsa dake Abuja. Wannan dai shine farkon taro da shugaban kasar yayi tun bayan dawowar shi daga hutun aiki ranar lahadin da ta gabata.

Allah Karawa Najeriya Albarka - Atiku Abubakar

Image
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, yayi wa iyalin sa da kasa Najeriya addu'ar neman albarka, inda ya rubuta a shafin sa na fesbuk kamar haka, " Allah ya ci gaba da karo albarkoki akan mu, iyalanmu da kasarmu a wannan rana ta Arafah. La ilaha ilallah, wahdahu la sharikallah, lahul mulk walahul hamd wa huwa ala kuli shayin Qadeer."

Kasar America Ta Girmama Limamin Da Ya Ceci Kiristoci A Jihar Plateau

Image
Kasar Amerika ta girmama tsohon limamin nan, Abdullahi Abubakar, wanda ya ceci sama da kiristoci 300 daga mahara a kauyen Nghar Yelwa da ke karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Plateau. An girmama limamin ne a wani taro da ofishin jakadancin amurka ya shirya a garin Jos inda suka roki sauran yan najeriya da su yi koyi da irin halin dattakon limamin.

In Ka Isa Ka Shigo Kano Ka Kaddamar Da Takara - Ganduje ya Kalubalanci Kwankwaso

Image
 Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalubalanci sanatan Kano ta tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso, da yazo Kano ya kaddamar da takarar sa in yana tunanin yana da dimbin magoya baya. Gwamnan ya kara da cewa kanawa ba za su tari Kwankwaso ba, kuma suna da damar zabar Dan takarar da suke ganin yafi dacewa. Ganduje ya ce ba su dauki Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasa ba, Buhari kawai suka sani kuma shi za su mara wa baya.

Shin Farfesa Osinbajo zai zama shugaban Najeriya?

Image
A halin yanzu 'yan Nijeriya da dama na nuna wa mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo matukar so irin wanda ba kasafai 'yan siyasa ke samu ba, a kasar da ba a kallon galibin 'yan siyasa da kima sosai. Ana yaba wa mataimakin shugaban kasar saboda yadda ya dauki kwararan matakai ba tare da wata-wata ba yayin da ya rika wa Shugaba Buhari a matsayin mukaddashin shugaban Nijeriya, lokacin hutun shugaban na kwanaki goma a baya-bayan nan. Yanayin hobbasa da kazar-kazar din mutumin, mai shekaru 61 a duniya, ya sha bamban da yanayin jinkiri da jan-kafa na Shugaba Buhari, mai shekaru 75 a duniya, wanda wasu 'yan kasar ke wa lakabi da ''Baba Go-slow'', wato ''Baba Mai nawa.'' Manyan jami'an gwamnatin Najeriya dai na cewa duk wani mataki da mataimakin shugaban kasar ko kuma shi kansa Shugaba Buhari ya dauka, abu ne na gwmnati guda babu wani bambanci, kuma dukkanninsu sun zo ne da manufofi guda da zimmar aiki tare. Amma duk da haka w...

An Kirkiro Sabon Manhajar Da Za Ta Rage Yawan Batan Alhazai

Image
Hukumar da ke kula da gudanar da aikin hajji ta najeriya, NAHCON, ta bayyana cewa ta kirkiro wata sabuwar manhaja da za ta rage yawan batan alhazai a lokacin aikin hajji. Hukumar ta ce fasahar na'ura mai kwakwalwar  ta GPS za ta dinga nuna wa alhazai taswirar wajen da suke da kuma inda suke nema. Manhajar tana dauke da shafin yanar gizo kuma an sanya ta a dukkan shemomin jihohin kasar ta yadda za a iya latsa duk wacce mutum ke nema daga ko ina, kamar filin Arfa da Muzdalifa da wajen jifa. Kuma nan take za ta nuna wa mutum taswirar inda zai bi ta manhajar Google map. Sai dai manhajar za ta dinga aiki ne kawai a wayoyin komai da ruwanka. Hukumar ta NAHCON ta ce ta kuma samar da wasu lambobin waya da alhazai za su iya kira ba dare ba rana domin neman taimako.

Zan Daure Barayi Da Yawa - Buhari

Image
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa aiki daga hutu shi ne daure barayi. Muhammad Buhari ya bayyana haka ne a hirar sa da gidan talbijin na NTA jim kadan bayan ya isa fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar. Bayan da aka tambaye shi game da abin da zai sa a gaba bayan ya yi hutun kwana goma, Shugaba Buhari ya ce "za mu daure barayi da yawa wadanda suka jefa mu cikin matsin tattalin arziki. Da ma na san ana sa ran zan yi hakan, kuma zan yi." Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa lokacin da yake yakin neman zabe. Buhari ya dawo Nigeria Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya ya rasu

Buhari ya dawo Najeriya

Image
Shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari, ya dawo gida Najeriya a yau bayan ya tafi hutun aiki na Kwana goma. Buhari ya samu tarba daga cincirindon magoya baya wadanda suka hada da gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello, da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Image
Shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari, zai dawo gida Najeriya yau bayan ya shafe kwanaki goma da ya tafi hutun aiki a Ingila. Shugaban kasar ya tafi hutun ran 3 ga watan August, inda ya bar mataimakinsa, Yemi Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa. Babban mai taimakawa shugaban kasar ta bangaren yada labarai, Garba Shehu, shi ya tabbatar da cewa Buhari 'zai dawo a yau' kodayake bai fadi takamaiman lokacin da zai dawo a yau din ba. Kofi Anan ya rasu kwankwaso ya hau jirgin saman daya daga cikin wadanda ya waje dan su koyi tukin Jirgi facebook din mu

Tsohon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan, Ya Rasu

Image
An sanar da mutuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya, Kofi Anan. Ya dai rasu a kasar Switzerland bayan wata  'yar gajeruwar rashin lafiya. Ana ganin mutuncin Kofi Anan a fadin duniya saboda rawar da ya taka a baya na tabbatar da zaman lafiya da daidaito. Ya kuma jagorancin majalisar dinkin duniya daga shekarar 1996 zuwa 2006, inda kuma ya Samu babbar kyauta ta bajinta (Nobel prize) akan Samar da zaman lafiya a shekarar 2001. Shafin mu na facebook

Kwankwaso Ya Hadu Da Matukin Jirgin Sama Da Ya Dauki Nauyin Karatun Sa A Hanyar Sa Ta zuwa Abuja

Image
Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya hau jirgin saman Azman yau da safe daga Lagos zuwa Abuja sai abin farin ciki ya faru: matukin jirgin yana daga cikin dalibai dari da Kwankwason ya tura makarantar koyon tukin jiragen sama da ke kasar Jordan dan su koyi tukin jirgin sama. Aminu Muhammad ya zama matukin jirgin saman Azman yau. Sanatan Kano din ya bayyana farin cikin sa akan hakan. Za a iya tuna cewa Kwankwason ya taba haduwa da wani matukin jirgin saman Azman din mai suna Hadi Sumaila a shekarar da ta wuce wanda shima matukin jirgin saman Azman din ne. facebook din mu

An Kama Manyan Dillalan Miyagun Kwayoyi Hudu A Jihar Gombe

Image
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, Shina Olukolu, ya bayyana cewa dakarun sa sun kama wasu dillalen miyagun kwayoyi hudu a jihar. Olukolu ya fadi haka ne ranar Alhamis a garin Gombe inda ya kara da cewa rundunar ta kama wadannan mutanen da miyagun kwayoyi da yawa a tare da su. Ya ce bayanan da suka samu game da su wadannan mutane ne ya sa suka sami nasarar kama su. ” Cikin kwayoyin da muka kama su da shi sun hada da kwayoyin Tramadol, Vallium, Dizapam, Exzol, Kodin da madaran su kodai’’. A karshe, Olukolu ya ce za su gurfanar da su a kotu da zaran an kammal bincike a kan su. Shiga Facebook din mu

Ganduje Ya Samu Sarauta A Jihar Abia - Zakin Da Yake Ba Da Kariya Ga Al'ummar Igbo

Image
Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu sarautar 'zakin da yake bada kariya ga al'ummar Igbo' da shugaban sarakunan gargajiya na kabilar Igbo da jihar Abia, Eze Eberechi Dick yayi masa a fadar Sa dake garin Abia. An ba gwamna Ganduje wannan sarautar ne saboda kokarin sa na tabbatar da adalci akan kabilu mazauna Jihar Kano ba tare da nuna musu bambanci, ko kyara ba. Shiga Shafin mu na Facebook

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Kama Wani Da Ya Kware Wajen Kera Bindigogi Yana Siyarwa Yan Fashi

Image
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da kama, Rabi'u Sulaiman, da ya kware wajen kera bindigogi yana sayarwa Yan fashin dake addabar jama'a a dajin falgore da titin Kano-Zaria-Kaduna. Kakakin Yan sandan ya rubuta a shafin Sa na facebook kamar haka " Wannan shine Rabiu Suleman Mutumin Kauyen Fadan Yalwa dake Karamar Hukumar Tudun Wada, shi kwararre ne wajen kera bindiga kala-kala yana sayarwa da Yan fashi dake addabar Jama’a a Dajin Falgore da Titin Kano-zuwa Zaria da Kaduna da sauran yankunan kudancin Kano. Mun kama shi da bindigogi da harsashi mai yawa kuma ana cigaba da gudanar da bincike". Shiga shafin mu na Facebook

'Zan Tsaya Takarar Shugaban K'asa A 2019 Idan 'Yan Najeriya Suka Bukaci Hakan — Hamza Al-Mustapha

Image
Tsohon dogarin Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewar zai iya tsayawa takarar shugaban 'kasar Najeriya a 2019 idan har 'yan Najeriya sun bu'kaci ya fito takara. "Ba zan bada sanarwar cewa zan yi takarar kujerar shugaban 'kasa ba. Amma idan mutane suka ce haka, to hakan shi ne muradinsu," Al-Mustapha ya faÉ—a a wata tattaunawa da aka yi da shi a Kaduna, bayan wani taro da ya yi da shuwagabannin wata 'kungiya mai rokonsa da ya tsaya takarar shugaban 'kasa a 2019 mai suna 'Eagle Eye Forum'. Al-Mustapha ya 'kara da faÉ—in: "Ni ba mutum ba ne mai matu'kar kwaÉ—ayin mulki. Da ni mutum ne mai kwaÉ—ayin hakan da tun a baya na rasa mutuncina. Amma idan mutane suka taru domin su yi magana, sannan suka yanke shawara da kansu, to wannan kira ne domin hidimta wa 'kasa." Ziyarci shafin mu na facebook

Amarya ta watsawa uwargidan ta tafasashshiyar miyar kuka a Jihar Jigawa

Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba ta na dakin girki sai uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan sai amaryar ta fara mayar mata da magana. Daga nan sai cacar baki ta kaure, ba tare da bata lokaci ba ne kuma amaryar ta dauki tukunyar miya tana tafarfasa ta watsawa uwargidan da danta a jikinsu. Bayan ta watsa musu miyar ne, sai amaryar kuma ta fara ihu na neman a kawo musu agaji. Mai magana da yawun yan sandan ya ce uwargidan da danta yanzu haka suna babban asibitin Dutse suna karbar magani, kuma duk jikinsu ya sabule musamman ma yaron. Kwamshinan yan sandan jihar, CP Bala, ya bayar da umarnin a kai amaryar da ta aikata lamarin sashen binciken kwakwaf domin gudanar da bincike da kuma yi mata hukuncin da ya dace. Majiyar mu ta BBC ta yi kokokarin jin ta bakin mijin matan wato Malam Hamza, amma wayarsa a rufe.

Kwankwaso Ya Ziyarci Gwamnan Jihar Akwa Ibom

Image
Ranar laraba jiya ne gwamnan jahar Akwaibom, Udom Emmanuel, ya tarbi mai niyyar tsayawa Takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a gidan gwamnatin da ke garin Uyo. Kwankwaso ya tabbatar wa gwamnan cewa lallai jama'ar Akwaibom din za su sake zaben gwamnan saboda dimbin ayyukan gina jihar da yayi.  Tsohon gwamnan Kano din kuma ya jijinawa gwamnan saboda dinbin jama'ar da ke bin Sa.

Ban Yanke Shawarar Fitowa Takarar Shugaban Kasa Ba Bar Yanzu - Saraki

Image
Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya bayyanawa manema labarai cewa har yanzu bai yanke shawarar tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin tutar PDP ba. Saraki wanda tsohon gwamnan jihar kwara ne ya nuna cewa a halin yanzu yana ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan makomar siyasarsa inda ya jaddada cewa zai iya samar da canjin da ake bukata a Nijeriya. Saraki ya kira majalisa taron gaggawa

Hukumar Zabe Ta Bukaci Naira Biliyan Shida Dan Ciyar Da Yan Sanda A Yayin Zaben 2019

Image
Hukumar zabe ta kasa ta bukaci naira miliyan shida dan ta ciyar da yan sanda a lokacin zaben 2019. Hukumar zaben ce ta gabatar da Wannan bukatar a cikin kasafin kudinta na zaben 2019 ga wakilan majalisa a yau. Yan majalisar sun bukaci shugaban hukumar zaben da ya kare muradin hukumar na bukatar wannan kudi a cikin zaman da su ke kan yi a halin yanzu.

Sunayen Sababbin Jam'iyyun Siyasa 23 Da Hukumar Zabe Ta Yiwa Rajista

Image
Hukumar zabe ta kasa ta bayar da sanarwar yiwa sabbin jam'iyyu rajista. Ga sunayen su Lamar haka: 1. Advanced Alliance Party (AAP) 2. Advanced Nigeria Democratic Party (ANDP) 3. African Action Congress (AAC) 4. Alliance for a United Nigeria (AUN) 5. Alliance of Social Democrats (ASD) 6. Alliance National Party (ANP) 7. Allied People’s Movement (APM) 8. Change Nigeria Party (CNP) 9. Congress Of Patriots (COP) 10. Liberation Movement (LM) 11. Movement for Restoration and Defence of Democracy (MRDD) 12. Nigeria Community Movement Party (NCMP) 13. Nigeria for Democracy (NFD) 14. Peoples Coalition Party (PCP) 15. Reform and Advancement Party (RAP) 16. Save Nigeria Congress (SNC) 17. United Patriots (UP) 18. United Peoples Congress (UPC ) 19. We The People Nigeria (WTPN) 20. YES Electorates Solidarity (YES) 21. Youth Party (YP) 22. Zenith Labour Party (ZLP) 23. Alternative Party of Nigeria (APN)

Yaro Dan Shekara 14 Da Ya Fito Takarar Gwamna A Amerika

  Yaro mai suna Ethan Sonneborn dan shekara 14 da bai kai shekarun kada kuri'a ba ko jan mota da kansa ya fito takarar gwamna a garin Vermont da ke Amerika. Yaron da ya ke neman jam'iyyar democrat ta tsayar da shi takarar gwamnan zai yi hakan ne saboda dokar yankin na su ba ta kayyade shekarun da mutum zai kai kafin ya tsaya takarar gwamnan ba. Sharadin kawai shine kowanne dan takara ya zama mazaunin garin na akalla shekara 4, shi kuma Soneburn shekarun Sa sha hudu a garin. Za su dai yi zaben fidda dan takara ranar talata shi da wasu manya guda uku.

Kalli Hoton Sabuwar Mortar Da Lukaku Ya Siya Naira Miliyan 48.

Image
Dan wasan gaba na Manchester United da Belgium, Rumelu Lukaku, ya se wa kansa sabuwar mota kirar marsandi akan kudi naira miliyan 48 (£102,000). An ga dan shekara 25 din ne yau a cikin sabuwar motar tasa a yau a garin Carrington dake kasar Ingila. Dan asalin kasar Congo din dai yana daukar albashin naira miliyan 97 duk mako.

Mai garkuwa da mutane da ya tafi dogon bacci bayan yasha tramadol ya rasu

Image
Hukumar yan sanda ta jihar Ondo ta bayar da sanarwar rasuwar Wanda ake zargi da garkuwa da mutane da ta kama a garin Owo, saboda ya sha kwayar tramadol ta yi masa karo.

Osibanjo Ya Ba Sufeto Janar Umarnin Yin Garambawul Ga Rundunar yan sanadan SARS

Image
Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo, ya ba Shugaban Rundunar 'Yan sanda ta kasa, Ibrahim K. Idris umarnin gaggauta yin garambawul ga rundunar yaki da miyagun laifuka ta SARS. Kakakin Mukaddashin Shugaban, Laolu Akande ya ce bin matakin ya zama dole sakamakon korafe korafe da ake ci gaba da yi game da yadda rundunar ke cin zarafin al'umma ba bisa ka'ida ba.

Hukumar Zabe Ta Tsawaita Wa'adin Rajistar Katin Zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa ( INEC) ta tsawaita wa'adin rajistar katin zabe da makonni biyu inda za a kammala shirin rajistar a karshen wannan wata na Agusta. Haka ma, Hukumar INEC ta yi wa wasu kungiyoyin jam'iyyu 23 rajista a matsayin jam'iyyun siyasa inda aka tsara mika masu satifiket a ranar Alhamis mai zuwa.

Jarumar Kanywood, Nafisa Abdullahi ta yi rashin mahaifiyarta

Image
Allah ya yi wa mahaifiyar kwararriya kuma shahararriyar jarumar Kanywood, Nafisa Abdullahi rasuwa.