Ado Gwanja Ya Angwance

Fitaccen jarumin nan da kan fito a fina-finan Hausa na masana'antar Kanyywood kuma mawaki da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamanin, Adamu Isa wanda aka fi sani da Gwanja ya angwance a yau asabar, 13 ga watan Oktoba 2018.
Mawaki Ado Gwanja dai ya auri masoyiyar sa ce mai suna Maimuna Kabir Hassan kuma an daura auren ne a garin Kano a yau asabar da misalin karfe 11 na safe a kan titin zuwa gidan Zoo.

Ado Gwanja yanzu yafi shahara ne a harkokin wakokin bukukuwa da wadanda suka shafi mata duk kuwa da cewa a wasu lokuttan yakan yi wakokin fina-finai da kuma na siyasa.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Tsohon gwamnan jahar Gombe Abubakar Hashidu ya rasu

Cristiano Ronaldo ya hadu da abokan wasan sa na Juventus a karon farko

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Yunkurin Kawo Tarnaki A Ayyukan Ci Gaban Kasa Da Gwamnati Ke Yi Wa Talakawa

Tsohon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan, Ya Rasu