1. KALLO: Mata suna aika sakonni da yawa ta hanyar kallo, kamar So, raini, tsoro, ba ruwana dakai da sauransu, kuma kowane ba sai an fassarawa mutum ba da ya gani yasan me ake nufi 2. KULAWA: Wannan na nufin ta nuna ta damu dashi a kowanne lokaci, ta hanyar kokarin jin halin da yake, lafiyarsa da kuma al'amuransa. Ko yana kusa da ita ko kuma nesa da ita. Idan abun murna ya sameshi ta tayashi idan na jaje ya sameshi ta jajanta masa. Ba shakka wannan yana nuna soyayya. 3. BIYAYYA: Mace ta rinka girmama namiji, abokansa da 'yan'uwansa a duk lokacin da zata mu'amalance shi ko su, a gaisuwa ne, a magana ce, a rubutaccen sako ne duk wadannan yana bukatar yaga ladabi acikinsu kada ta rinka yi masa tsiwa da rashin kunya da sauran dabi'u da zasu nunawa mutum ba a dauke shi abakin komai ba. 4. HAKURI: Babban abinda yafi bada wahala a mu'amala kuma a kafi jarraba mutum akai shine hakuri, ya zamanto namiji ya gamsu da hakurin mace ta kowace hanya kar ta rinka yi masa kok...