Posts

Kwankwaso ya je jihar rivers Dan yiwa Gwamna Wike ta'aziyya

Image
Mai neman takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya cancanci zango na biyu saboda dimbin ayyukan raya kasa da yayi a jihar. Tsohon gwamnan jihar Kano din yayi wannan bayani ne a gidan gwamnatin rivers da ke fatakot a daren litinin a yayin da yaje ta'aziyyar rasuwa wani kusa a gwamnatin ta rivers. Kwankwaso ya gana da Obasanjo a jihar Ogun

Buhari zai fito takarar zabe tare da Osinbajo a 2019 - Fadar shugaban kasa

Image
Fadar shugaban kasa yau litinin ta ce mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo zai cigaba da zama abokin takarar shugaban kasa Muhammad Buhari a zaben 2019. •Osinbajo ya tsige lawal Daura daga mukamin sa Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafofin yada labarai, Garba Shehu, shi ya tabbatar da haka ga manema labarai da ke fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Abu ne me matukar wuya Ganduje ya sake cin zabe a Kano~ Tsohon mataimakin gwamna Hafiz Abubakar

Image
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano mai da ya sauka kwanannan, Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa duba da irin yadda abubuwa ke gudana a siyasar jihar Kano, abu ne me matukar wuya ace Ganduje ya sake cin zabe a shekarar 2019. Farfesa Hafiz yayi wannan bayani ne a lokacin da yake hira da jaridar The Punch. Ya kara da cewa, PDP ce zata samu nasara a jihar a zabe me zuwa domin kuwa da yawa wadanda ke zagaye da gwamnan sun gaji da zama a APC saboda rashin adalcin da ake musu suna ta komawa PDP. Yace 'yan majalisar jihar ma ba'a barsu a baya ba wajan canja shekar inda ya kara da cewa yana da yakinin tsohon gwamnan jihar, Sanata Kwankwaso ne zai samu tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a PDP a zaben 2019.

Wani jariri maraya da iyayen sa su ka gudu su ka barshi an sa masa suna Muhammad Buhari a gidan marayu

Image
Wata mai aikin daukar hoto, Fatima Abubakar, ta nuna hoton wani kyakkyawan jariri maraya da ba a san iyayen sa ba Wanda kuma yana gidan marayu na Maiduguri a halin yanzu. An dai sa masa sunan shugaban kasar Nigeria, Muhammad Buhari.

Cutar kwalara da ta barke a Jamhuriyyar Nijar inda ta hallaka kusan mutane 19.

Kimanin mutane dubu 1,168 ne suka kamu da cutar a gundumar Madarunfa ta jahar Maradi da ke yankin kudancin kasar. Sama da wata daya ke nan da aka samu barkewar wannan cuta a wannan yanki, kuma cikin wadanda lamarin da cutar ya shafa yara kanana sun fi yawa. Dr Alhaji Ibrahim Tasiu shi ne darakatan kiwon lafiya a gundumar ta Madarunfa kuma ya shaidawa BBC cewa daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa yanzu kusan mutane 19 suka mutu. Mutanen da suka kamu da wannan cuta ta amai da gudawa na kwance a babban asibitin birnin Maradi ne, kamar yadda hukumar jin kai ta Majalasar Dinkin Duniya wato OCHA ta sanar. Rahotanni sun bayyana cewa a garin N'Yelwa ne aka fara samun mutum na farko da ya kamu da cutar tun a farkon watan Yuli da ya wuce.

Za a yi babbar sallah ran talata a Kano

Babban kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ranar Talata 21 ga wannan watan ne ranar babbar Sallah a Najeriya. Kwamitin ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana dalilinsa na yin haka: "A kan batun cewa Saudiyya ta bayyana ranar Dhl Hijjah da ta bambanta da wanda muka riga muka bayyana, kwamitin ganin wata ya tuntubi babban kwamitin Fatawa na kasa a shekarun baya, kuma an fitar da wata Fatawa mai cewa ya kamata mu rika bin hukuncin ganin watan da kasar Saudiyya ta yanke na Dhul Hijjah saboda muhimmancin hawan Arafat." Wannan sanarwar ta ci karo da sanarwar farko da kwamitin ya fitar. Sanarwar kwamitin ta cigaba da cewa, "A kan haka ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, bayan ya tuntubi kwamitin Fatawa da kwamitin ganin wata da sauran malaman addini har da sarakunan gargajiya, ya bayyana Lahadi 12 ga watan Agusta 2018 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah 1439H."

Baiwa 11 Da Allah Ya Yi Wa Sheik Ja'afar Yayin Rasuwarsa

Image
Baiwa 11 Da Allah Ya Yi Wa Sheik Ja'afar Yayin Rasuwarsa Daga Rabi'u Maiwaya Limawa 1. SHAHADA: Ya yi Shahada iri daya da ta Sayyidina Umar (R.A) 2. Ya rasu ranar Juma'a: Rasuwar Ranar Juma'a alama ce da ake kyautata wa Mutum zato ya samu dacewa. 3. Mahaddacin Alkur'ani ne: Ana kyautata zaton duk wanda ya haddace Alkur'ani Mai Girma ya kuma kiyaye shi ya yada shi. Zai samu rabauta ranar Lahira. 4. Kisan Gilla: Duk Muminin da aka yi wa kisan gilla ana sa ran laifukan sa sun rataya a wuyan wanda ya kashe shi. 5. Ya cika da kalmar SHAHADA: Kafin rasuwar sa an ji shi ya na maimaita kalmar La ila ha illallah Muhammadur Rasulullah 6. Dandazon Mutanen da suka halarci jana'izarsa: Ana kyautata zaton duk mamacin da mutane 40 suka halarci jana'izarsa wadanda ba sa shirka zai samu dacewa. 7. Ya rasu ya na Sallar Asuba. Sallar Asuba na daya daga cikin Sallah mai madaukakiyar daraja. 8. Limami ne shi: Jagorancin Sallah wata babbar baiwa ce da ke kusanta Bawa...

Kwankwaso ya gana da Obasanjo a jihar Ogun

Image
Yau Kwankwaso ya je jihar Ogun inda ya hadu da magoya bayan sa, daga nan kuma ya je su ka gana da tsohon shugaban kasar Nigeria, chief Olusegun Obasanjo. Kwankwaso shine dan takarar shugaban kasar da Obasanjo yafi nutsuwa da shi dan kada Shugaban kasa Muhammad Buhari a zabe mai gabatowa.

Kasar Saudi Arabia Ta Fitar Da Ranar Da Za 'ayi Arfa.

Image
Babbar ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulinci ta kasar Saudi Arabia ta bada sanarwar ganin watan zulhajji yau asabar. Saboda haka gobe lahadi zai zama 1 ga watan Zulhajji, wanda yayi daidai da 12 ga watan Augusta 2018. Abisa wannan ne ma'aikatar ta bada tabbacin Ranar litinin 20 ga watan Augusta 2018 zai kasance Ranar Arfa wato 9 ga wata Zulhajji 1439 .

Sakamakon zaben yau daga mazabar Buhari ta Daura.

Image
Buhari ba ya kasar amma mutanen mazabar sa sun tula ma dan takarar jam'iyyar sa kuri'u. PDP kuri'a daya jal ta samu a mazabar baba Buhari. Kalli hoton sakamakon zaben da vanguard news su ka wallafa.

Wannan shine Tanmay Bakshi, yaron da yake aiki a Google kuma suke biyanshi albashin naira miliyan dari hudu da hamsin a shekara

Image
Tanmay Bakshi, dan shekara sha hudu, kwararre kuma mai hazaka akan kera manhajar komfyuta. Yayi aiki da Watson da kuma IBM a baya , yanzu kuma yana aiki da Google inda suke biyan sa albashin naira miliyan dari hudu da hamsin duk shekara. Za mu sa ido muga sabuwar fasahar da zai kirkira zuwa karshen shekarar nan. Lallai wannan shine dan baiwa

Kungiyar da ke shirya wasan zakarun turai (UEFA) ta fitar da sunayen wadanda su ka fi kwazo a kakar da ta gabata

Image
 Kungiyar da ke shirya wasan zakarun turai (UEFA) ta fitar da sunayen wadanda su ka fi kwazo a kakar da ta gabata: Sunayen yan gaba da su ka fi taka rawa: - Cristiano Ronaldo (Juventus) - Mohamed Salah (Liverpool) - Lionel Messi (Barcelona) Sunayen yan tsakiya da su ka fi taka rawa: - Luka Modric (Real Madrid) - Toni Kroos (Real Madrid) - Kevin De Bruyne (Manchester City) Sunayen yan baya da su ka fi taka rawa: - Sergio Ramos (Real Madrid) - Marcelo (Real Madrid) - Rapheal Varane (Real Madrid) Sunayen masu tsaron gida da su ka fi taka rawa: - Alisson Becker (Liverpool) - Keylor Navas (Real Madrid) - Gianluigi Buffon (PSG) Za a sanar da sunayen wadanda su ka ci nasara a yayin tsara jadawalin kakar was an zakarun turai na gaba da za a yi a Monaco ran talatin ga watan August.

Osinbajo, Oshiomole da Ganduje sun je jihar Katsina dan taron APC

Image
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Gwamna Ganduje da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adam Oshiomole, sun je karamar hukumar Isa dake jihar Katsina dan taron neman magoya baya akan Sake  zaben sanata da ya ke gabatowa. Dubban mutane sun halarci taron inda cikin farin ciki mata da maza su ka dinga ihun "APC,APC" "Nigeria said baba, Katsina sai masari"

Wani hoto da ya nuna Ganduje na ragewa Kwankwaso hanya a kan vespa dinshi a shekarar 1981

Image
Wannan wani tsohon hoto ne da aka dauka a shekarar 1981. Ya nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da sanatan Kano ta tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso suna tafiya a kan vespa da kayan makaranta. Ganduje ne ke jan babur din.

"Dole saraki ya sauka": matasan arewa sun yi zanga-zanga yau a Kano

Image
Kungiyar matasan arewa sun gudanar da zanga-zanga akan neman saraki ya sauka daga shugabancin majalisa. An ga hotunansu suna daga kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce iri-iri na neman sarakin ya sauka.

Pogba ya amince da tayin albashin zunzurutun kudi naira miliyan dari da arba'in da bakwai- duk sati da Barcelona su ka yi masa

Image
Paul Pogba zai iya rattaba hannu ga zakarun spain, kungiyar Barcelona a cikin sa'o'i ashirin da hudu masu zuwa idan Manchester United su ka amince da yarjejeniyar canja shekar dan wasan. An samu rahoton cewa Paul Pogba ya amince da tayin albashin naira miliyan dari da arba'in da bakwai- duk sati da Barcelona su ka yi masa. Pogba ya bayyana cewa yana son barin kungiyar Manchester United zuwa Barcelona ko da yake Manchester din ba su shirya rabuwa da shi ba.

Kwankwaso ya karbi katin jama'iyya daga jam'iyyar PDP ta Kano

Image
Mai girma sanatan Kano ta tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi katin jam'iyyar PDP a yau. Shugaban jam'iyyar na jihar Kano, Senator Mas'ud El-jibril Doguwa ne ya bashi katin.  

Gwamnan jihar Borno ya dauki nauyin karatun dalibin da yayi fice a jarrabawar JAMB

Image
Hukumar dake shirya jarrabawar shiga jami'ar wato JAMB, ta bayyana Galadima Israel Zakari da ke Biu, jihar Borno, a matsayin Wanda ya fi kowa yawan maki a jarrabawar da aka yi ta shekarar 2018, inda ya samu maki 364 a zaman jarrabawar da yayi a jihar Ogun. Gwamnan Borno, Kashim shettima, ya gayyaci dalibin ran talata inda ya bayyana Dakar nauyin karatun digirin  dalibin a jami'ar Covenant na tsawon shekara biyar.

Jami'ar Bayero ta Kano ta kori dalibai talatin da uku akan samun su da magudin jarrabawa

Image
      Hukumomin jami'ar Bayero ta Kano sun kori dalibai talatin da uku saboda zargin shigarsu cikin hanyoyi daban-daban na magudin jarrabawa a yayin jarrabawar zangon farko na shekarar 2017/18. Bayani da yake kunshe da sa hannun mukaddashin darakta akan jarrabawa da ajiye bayanai, Hajiya Amina Abdullahi, ya tabbatar da amincewar hukumar dattijan jami'ar na korar daliban da abin ya shafa. Jami'ar ta ce dalibai coma sha biyu za su maimaita shekarar karatun, saba' in da biyu kuma an gargade su. " Haka kuma, an wanke dalibai biyu daga kowanne laifi, yayin da dalibai biyu kuma a jingine hukunta su har said an kammala bincike.

Osinbajo ya kori shugaban hukumar tsaro ta farin kaya wato Lawal Daura

Image
Mukaddashin shugaban kasar Nigeria, farfesa Yemi Osinbajo, ya kawo karshen wa'adin mukamin shugaban hukumar tsaro ta farin kaya wato Lawal Daura. Babban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa ta bangaren yada labarai da kafofin sadarwa, Laolu Akande,  ya bayyana hakan a shafin sa na twitter.