Posts

Sabon labari

Ado Gwanja Ya Angwance

Image
Fitaccen jarumin nan da kan fito a fina-finan Hausa na masana'antar Kanyywood kuma mawaki da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamanin, Adamu Isa wanda aka fi sani da Gwanja ya angwance a yau asabar, 13 ga watan Oktoba 2018. Mawaki Ado Gwanja dai ya auri masoyiyar sa ce mai suna Maimuna Kabir Hassan kuma an daura auren ne a garin Kano a yau asabar da misalin karfe 11 na safe a kan titin zuwa gidan Zoo. Ado Gwanja yanzu yafi shahara ne a harkokin wakokin bukukuwa da wadanda suka shafi mata duk kuwa da cewa a wasu lokuttan yakan yi wakokin fina-finai da kuma na siyasa.

Yau Ce Ranar Zuciya Ta Duniya

________________ Zuciya wani sashin jikin ɗan'adam ne da ke harba jinin da ke ɗauke da iskar "Oxygen" da sinadaran abinci zuwa dukkan sassan jiki domin cigaban rayuwa. Haɗaɗɗiyar ƙungiyar lura da masu ciwon zuciya ta duniya ce ta ware ranar 29 ga watan Satumba na kowacce shekara domin gangamin wayar da kai dangane da kiyaye lafiyar zuciya. Binciken ƙwararru ya tabbatar da cewa motsa jiki ko atisaye na taka muhimmiyar rawa wajen: 1) Gina tsokar zuciya da share hanyoyin jini. 2) Rage hawan jini 3) Daidaita suga a cikin jini 4) Ƙone tararren kitse a cikin jini da sauran sasan jiki. 5) Daidaita sinadaran da ke angiza bugawar zuciya, da dai sauransu. Sai dai sau dawa za ka ji masana harkokin lafiya suna cewa a motsa jiki, ba tare da keɓe wanne irin motsa jiki ko atisaye ne ke da alfanu ga lafiyar jikin ba. Tuntuɓi likitan Fisiyo a yau domin neman shawarwari kan fara motsa jiki/atisaye domin dacewa da alfanun da aka ambata a sama. https://mobile.facebook.com/Physi...

Zanga Zangar Ranar Ashura : Jami'an Tsaro Sun Bude Wuta Akan 'Yan Shi'a.

Image
Rahotanni daga birnin Zariyan Jihar Kaduna sun bayyana cewar rundunar 'yan Sandan jihar sun bude wuta gami da watsa barkonon tsohuwa akan dubban 'yan shi'a Maza da Mata wadanda ke gudanar da zanga zangar ranar ashura, domin nuna bakin ciki da alhinin su akan kisan da akayiwa jikan Annabi wato Sayyidina Hussain a Karbala. Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar, tun da sanyin asubahin ranar yau ce 'Yan Shi'an suka yi dafifi suka cika birnin na Zazzau sannan suka rurrufe hanyoyi suka hana jama 'a gudanar da harkokin su na yau da kullum, suna rera wakokin tsinuwa da La'antar wadanda suka aiwatar da kisan Sayyidina Hussain, hakanan kuma sun cigaba da La'antar wadanda suka kira a matsayin shugabanni masu koyi da azzaluman farko, inda suka rinka kiran sunan Buhari da Buratai da El Rufai suna tsine musu, lamarin da ya haifar da hatsaniya da kuma tarzoma a birnin.

Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000

Image
Wani Mutum Ya Kona Fuska Da Nonon 'Yar 'Dan Uwansa Da Dutsen Guga Akan Zargin Ta Sace N3000 Wani Mr. Sunday Ekpong ya kona yarinya 'yar shekara 13 da dutsen guga a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa akan batan kudin makocin su. Wanda ya yadda labarin a Facebook dinshi mai suna Efibre, ya cemakocin yaga kudin nasa da suka bata daga baya a inda ya ajiye su . Ranar Galata 5/9/2018 aka zargi karamar yarinyar da sace N3000 daga makocin su. Bayan bincike da barazana daga kawunta yarinyar ta dage akan cewa bata saci kudi ba. Kawunnata sai ya fara yi mata dukan rashin imani yana sa ta fito da kudi amma yarinyar ta dage akan bata saci kudi ba. Daganan ya cire mata kaya ya dauko dutsen guga mai zafi ya dinga danna mata a fuskar ta da nonon ta akan cewa ba zai daina ba har sai ta yarda ta saci kudin. Yarinyar ta amince da hakan dan ta samu saukin azabtarwar da yake mata. Abin bacin rai akan labarin shine makocin yaga kudin nasa a inda ya ajiyesu. Shi kuma kawun nata ya kaita asi...

Hoton Messi 'Ya'yansa

Image
Hoton Messi 'Ya'yansa Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya sa hoton shi tare da 'ya'yan sa a Instagram dinshi yau.

Shekarau Ya Koma APC

Image
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP Zuwa APC. Dan tabbatar da wannan labari ga jaridar Daily Trust da safen nan, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u Sule, ya bayyana cewa tsohon gwaman ya yanke shawaran fita daga jam'iyyar ne bayan muhawara tsakaninsa da mabiyansa. Sule ya kara da cewa babu yadda zai yiwu su cigaba da kasancewa cikin PDP duba ga yadda shugabancin jam'iyyar ta kasa ya karkata kan Kwankwaso sabanin sauran shugabannin PDP a jihar.

Mutanen Da Hukumar Zabe Ta Yiwa Rajista Kawo Yanzu

Image
Sabon jerin adadin wadanda hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta yiwa rajista da suka cancanci kada kuri'a a zaben 2019. Kudu maso gabas Abia 1,481,191 Anambra 1,758,220 Enugu 1,301,185 Imo 1,611,715 Ebonyi 876,249 Adadi = 7,028,560 ------------------------------------------------------------------ *Kudu maso yamma:* *Lagos 6,247,845* *Ogun 1,869,326* *Osun 1,293,967* *Ondo 1,558,975* *Ekiti 750,753* *Oyo 2,577,490* *Adadi=14,298,356* ------------------------------------------------------------------ Kudu maso kudu: Edo 1,412;225 Delta 1,900,055 Bayelsa 472,389 Akwa Ibom 1,714,781 RIvers 2,419,057 C/Rivers 1,018,550 Adadi 8,937,057 ------------------------------------------------------------------ Arewa ta tsakiya: Benue 1,415,162 Kogi 1,215,405 Kwara 1,115,665 Nassarawa 1,224,206 Niger 721,478 Plateau 1,983,453 Adadi 7,675,369 ------------------------------------------------------------------ Arewa maso gabas: Adamawa 1,714,860 Bauchi 1,835,562 ...

Illar Shan Magunguna Barkatai

Abin da ya kamata ka sani dangane da shan magungunan ciwon jiki barkatai. __________________ Ɗabi'ar shan magungunan ciwon jiki da gaɓɓai ɗabi'a ce da ta zama ruwan dare, sai dai jinsin magungunan rage ciwo, raɗaɗi, ko zafin jiki da ake cewa NSAIDs (Nonsteroidal Anti-inflammatory Drugs) ba sune mafita ga masu fama da ciwon jiki ba, kamar masu fama da ciwon baya, ciwon wuya, ciwon gwiwa da sauransu. Domin irin waɗannan ciwuka suna faruwa ne sakamakon saɓanin zaman ƙashi, jijiya da tsoka a jiki. Saboda haka ciwon jiki ko ciwon wata gaɓa na faruwa ne a matsayin alama ko gargaɗi cewa an sami saɓani tsakanin tsoka, ƙashi ko jijiya. Wannan ne yasa ko mutum ya sha maganin ciwon jiki da zarar ƙarfin maganin ya ƙare a cikin jini to wannan ciwo zai dawo har sai an sake shan wani maganin kuma. A taƙaice jinsin waɗannan magunguna ba sune haƙiƙanin matsalar ciwo ba dangane da ciwukan jiki da suke da asali daga jijiya, ƙashi da tsoka. Haka nan waɗannan magunguna suna a matsayin shamaki ...

UEFA Ta Fitar Jadawali. Modric Ya Yi Fice

Image
Hukumar da ke gudanar da wasan zakarun turai, UEFA, ta fitar da jadawalin rukunan wasan da za a yi (champion league) a kaka mai zuwa. Hukumar ta kuma zabi dan kasar Croatia dake buga wa Real Madrid wasa, Luka Modric', a matsayin dan kwallon da yayi fice. Cristiano Ronaldo ne ke biye masa sai kuma Mohammed Salah a matsayin na uku Group A Atlético Madrid, Dortmund, Monaco, Club Brugge Group B Barcelona, Tottenham, PSV, Inter Milan Group C PSG, Napoli, Liverpool, Crvena zvezda Group D Lokomotiv Moskva, Porto, Schalke, Galatasaray Group E Bayern Munich, Benfica, Ajax, AEK Anthens Group F Man. City, Shakhtar Donetsk, Lyon, Hoffenheim Group G Real Madrid, Roma, CSKA Moskva, Plzeň Group H Juventus, Man Utd, Valencia, Young Boys

Saraki Zai Tsaya Takara

Image
Shugaban majalisar dattijai na Najeriya, Dr. Bukola Saraki, Ya bayyana aniyarsa ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2019, Inda Ya sha Alwashin Kai Najeriya ga nasara Shugaban majalisar na Dattawan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, a yayin taron tattaunawa da matasa da aka gudanar a otal din Sheraton da ke Abuja.

Yan Takarar Shugabancin Kasa 42

Image
      Adadin wadanda suka bayyana aniyar su ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019 ya kai 42 zuwa yanzu.  Ga sunayen su: 1. Kingsley Moghalu 2. Sule Lamido 3. Donald Duke 4. Kabiru Tanimu Turaki 5. Ahmed Mohammed Makarfi 6. Ibrahim Dankwambo 7. Muhammadu Buhari 8. Fela Durotoye 9. Funmilayo Adesanya-Davies 10. Remi Sonaiya 11. Thomas-Wilson Ikubese 12. Omoyele Sowore 13. Enyinnaya Nnaemeka Nwosu 14. Ahmed Buhari 15. Adesanya Fegbenro-Bryon 16. Charles Udeogaranya 17. Mathias Tsado 18. Eniola Ojajuni 19. Olu James Omosule 20. Tope Fasua- Anrp 21. Elishama Rosemary Ideh 23. Usman Ibrahim Alhaji 24. Datti Baba Ahmed 25. Adamu Garba 26. Chris Emejuru 27. Oluwaseyitan Lawrence Aletile 28. Omike Chikeluba Lewis 29. Ibrahim Ladaja 30. Omololu Omotosho 31. Fidelis Akhalomen Lawrence Ekoh 32. Alhaji Atiku Abubakar 33. Ibrahim Shekarau 34. Professor Iyorwuese Hagher 35. Chike Ukaegbu 36. Attahiru Bafarawa 37. Rabiu Musa Kwan...

Kwankwaso Ya Kaddamar Da Takarar Sa

Image
Sanatan Kano ta tsakiya, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kaddamar da takarar sa ta neman shugaban kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP. Tsohon gwamnan Kano din ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar ga dubban magoya bayan sa da akasarin su ke sanye da jar hula infa akayi taron a Cida Hotel da ke Jabi and garin Abuja.