Ado Gwanja Ya Angwance
Fitaccen jarumin nan da kan fito a fina-finan Hausa na masana'antar Kanyywood kuma mawaki da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamanin, Adamu Isa wanda aka fi sani da Gwanja ya angwance a yau asabar, 13 ga watan Oktoba 2018. Mawaki Ado Gwanja dai ya auri masoyiyar sa ce mai suna Maimuna Kabir Hassan kuma an daura auren ne a garin Kano a yau asabar da misalin karfe 11 na safe a kan titin zuwa gidan Zoo. Ado Gwanja yanzu yafi shahara ne a harkokin wakokin bukukuwa da wadanda suka shafi mata duk kuwa da cewa a wasu lokuttan yakan yi wakokin fina-finai da kuma na siyasa.