Yau Ce Ranar Zuciya Ta Duniya


________________
Zuciya wani sashin jikin ɗan'adam ne da ke harba jinin da ke ɗauke da iskar "Oxygen" da sinadaran abinci zuwa dukkan sassan jiki domin cigaban rayuwa.
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar lura da masu ciwon zuciya ta duniya ce ta ware ranar 29 ga watan Satumba na kowacce shekara domin gangamin wayar da kai dangane da kiyaye lafiyar zuciya.
Binciken ƙwararru ya tabbatar da cewa motsa jiki ko atisaye na taka muhimmiyar rawa wajen:
1) Gina tsokar zuciya da share hanyoyin jini.
2) Rage hawan jini
3) Daidaita suga a cikin jini
4) Ƙone tararren kitse a cikin jini da sauran sasan jiki.
5) Daidaita sinadaran da ke angiza bugawar zuciya, da dai sauransu.
Sai dai sau dawa za ka ji masana harkokin lafiya suna cewa a motsa jiki, ba tare da keɓe wanne irin motsa jiki ko atisaye ne ke da alfanu ga lafiyar jikin ba.
Tuntuɓi likitan Fisiyo a yau domin neman shawarwari kan fara motsa jiki/atisaye domin dacewa da alfanun da aka ambata a sama.


https://mobile.facebook.com/PhysioHausa

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Buhari Zai Dawo Najeriya A Yau

Dalilin da yasa Hafizu Abubakar ya ajiye makamin sa na mataimaki na - Ganduje

Hafiz Abubakar ya ajiye makaminsa na mataimakin gwamnan Kano

Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari zai lashe a zaben 2019