Birtaniya Ta Dawowa Da Najeriya £70m

Birtaniya ta dawowa da Najeriya £70m, ta yi alkawarin dawo da kari anan gaba
Gabanin zuwan Firam Ministan Birtaniya nan Najeriya, gwamnatin kasar ta dawowa da Najeriya da wasu makudan kudade da wani ma’aikacin gwamnatin Najeriya ya kai kasar.
Kasar Birtaniya ta dawowa Najeriya da makudan kudi £70m da aka kwato daga hannun wani barawon gwamnati da ya sace kuma wata kotun Italiya ta kama shi.
Jakadan Birtaniya zuwa Najeriya, Mr Paul Arkwright, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Yace:“Akwai wata karar kotun Italiya da wani mutum, Wani kashin kudin na ajiye kasar Birtaniya kuma an maido da kudin Najeriya kwanan nan.
Saboda hakane aka dawo da Fam milyan 70."
Amma jakadan Mr Paul Arkwright,ya ki bayyana sunan dan Najeriyan da ya kai kudin Najeriya wajen.
Ya ce dai za’a dawo da karin kudi inda ya jaddada cewa kasarsa na aiki da gwamnatin Najeriya domin kara saurin gudun yadda za’a dawo da su.

Comments

Labarum da su ka fi Jan hankalin makarantan mu

Zan Daure Barayi Da Yawa - Buhari

Adadin masu neman shugabancin kasa ya kai 46 a halin yanzu, karanta sunayen su

Illar Shan Magunguna Barkatai

Buhari ya bukaci magoya bayansa da su dakatar da yakin neman zaben sa a halin yanzu